Hausa NewsHealthNews

NAFDAC zata hana shigowa da siyar da man bilicin a nigeria

Hukumar NAFDAC ta kudiri anayar hana shigowa da siyar da man shafawa me saka hasken fata wanda muke kira da bilicin a nigeria gaba daya.

wanda ta nuna hakan yana iya kasancewa illa ko barazana ga lafiyar fata dama jiki gaba daya wajen mutanen nigeria.

kamar inda kowa ya sani dai wan nan hukuma tana yaki ne da duk wani gurbatacen abin ci kona sha ko magani da bashi da kyau a cikin kasa nigeria wanda aka shigo dashi ko kuma aka hada shi acikin kasa nigeria.

a yanzu haka dai mutane suna ta fadin albarkacin bakin su akan wan nan hukuncin da hukumar NAFDAC ta dauka akan manshafawa me saka hasken fata musamman ga yanmata wanda hakan ya zama ruwan dare a birni da kauye da kuma sako da lungu a cikin nigeria gaba daya.

fifa world cup 2022

inda wasu suke ganin cewa hakan zai saka yanmata da yawa cikin tashin hankalin idan andena siyar da wan nan mai ko kuma aka saka doka akansa yayi wuya ya zama ba’a iya siyar dashi sai a boye hakan zai saka shi yayi tsada.

a hasashe wasu kuma suna ganin shi wan nan mai idan aka fara shafa shi ba’a denawa idan kuma kayi sakaci ka dena to tabbas fatan jikin mutum zata lalace tayi dabbare-dabbare.

to a yanzu haka dai yanmata da yawa sun shiga tashin hankali a dalilin zaa hana siyar da wan nan mai na shafawa me kara hasken fata a fadin nigeria

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page