News

‘Yan Bindiga: Zamu Sace BUHARI Da El-Rufai A Wani Sabon Bidiyo

‘Yan Bindiga: Zamu Sace BUHARI Da El-Rufai A Wani Sabon Bidiyo

Makonni bayan farmakin da aka kaiwa jerin motocin shugaba Muhammadu Buhari a jihar Katsina.

Yan ta’adda sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasar na Najeriya Muḥammadu Buhari.

Also Read: Kalla video Maryam yahaya tana rawa gaban larabawa a Dubai suna manna mata kudi a jikinta

‘Yan Nigeria Kukan Dadi Sukeyi Inji Buhari

An dai kai farmaki kan tawagar tsaron shugaban kasar a hanyarsu ta zuwa mahaifar Buhari da ke Daura kafin bikin Sallah.

Mutane biyu sun jikkata a yayin harin wanda akace fadar shugaban kasar ta dakile.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, cikin sabon bidiyon da suka saki,

yan bindigar wadanda suka sace fiye da fasinjoji 60.

A jirgin kasar Kaduna-Abuja a ranar 28 ga watan Maris,

sunyi barazanar sacewa da kuma halaka Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Yan ta’addan sun kuma bugi kirjin cewa sai sun lalata kasar, sun kuma ce sai sun kashe sauran fasinjojin jirgin kasa,

Wa’inda da suka rage a hannunsu sannan su siyar da sauran.

A bidiyon da jaridar Leadership ta wallafa a Youtube, an jiyo daya daga cikin yan ta’addan na cewa;

“Kasar nan sai mun lalatata gaba daya, da mutanen cikinta gaba daya
Idan za kuzo kuyi addini, kuzo kuyi amma muna nan muna kafa kanmu, addinin nan saimun yada ta a ko’ina”.

Barazana Ga EL-RUFAI Da BUHARI – Yan Bindiga

“Ka sani sai mun kama ka da hannun mu, mun kawo ka dajin nan mun yanka ka,

mun Nemo El-Rufai a Kaduna gaba daya babu shi”.

Ku sani gani acikin dajin nan, kuma ku dube ni da kyau ba wai baku sanni ba.

Kun sanni kun tura hotona ga jami’an tsaro gaba daya wai duk inda aka ganni a kama ni.

Ku sani gani acikin dajin nan, kuma ku dube ni da kyau ba wai baku sanni ba.

Kun sanni kun tura hotona ga jami’an tsaro gaba daya wai duk inda aka ganni a kama ni.

Duk inda na ganku, nima nasa a nemo min ku, nima ina so in kama ku gaba dayanku, sannan kuma in kashe ku.

Yaci Gaba Da Cewa:

Kamar yadda muka siyar da yan matan Chibok, haka za mu siyar da wadannan a matsayin bayi.

“Idan kun ‘ki yarda da bukatar mu za mu kashe wadannan sannan mu siyar da sauran.
Da izinin Allah, El-Rufai, Buhari, sai mun kawo ku nan. Inji shi”.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page