Life Style

(Kannywood) Kotu ta daure wata Babban Jaruma

Kotu ta dare jaruman kannywood sadiya haruna a gidan yari daurin da babu tara a cikin ta

KOTU TA DAURE JARUMAN KANNYWOOD

(kotu ta daure wata baban jaruman kannywood) Wata  daya daga cikin Jaruman Kannywood kuma me saida kayan mata Sadiya Haruna, kotu ta yanke mata hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ba tare da zabi na biyan tara ba inda kotun ta samu sadiya haruna da laifin bata sunan abokin aikinta, Jarumin kannywood Isa A Isa.

LEFIN DA SADIYA HARUNA TAYI

Kotu ta tuhumi jarumar kannywood Sadiya haruna da laifin bata sunan Isa a Isa a cikin wani bidiyo nata da ta saki acikin shafukanta na sada zumunta inda video ya karade shaafukan sada zumunta daban daban.

ABINDA ALKALI YA YANKE HUKUNCI

Me shari’a Da yake karanta hukuncin nasa, Mai shari’a Muntari Dandago, yace tabbas ya samu jarumar sadiya haruna da laifukan da ake tuhumarta da ita, don haka dole ya hunta ta.

HUJJA AKAN ABINDA JARUMAR TA AIKATA

Jaruma sadiya haruna dai tayi zage zage da kage da kazafi  inda aka samu hakan cikin wani video nata da ta saka a cikin shafukan sada zumunta nata haka nan tayi ma Isa a isha kazafi da zama dan luwadi, dan iska kuma mai neman mata

LALATAN DA ISA A ISA SUKAYI DA SADIYA HARUNA

Sadiya Haruna tayi ikirarin cewa jarumin kannywood, Isa A Isa ya bukaci yiyi lalata da ita wato zina taki yarda da bukatan shi ta bayyana hakan ne a cikin shafukanta na sada zumunta.

GARGADI AKAN JARUMAN KANNYWOOD

Alkalin kotun ya kuma bayyana cewa idan har jaruma Sadiya Haruna ta ci gaba da bata sunan Isa a isa, tabbas kotu zata dauki mataki me tsauri akan jaruma satiya haruna inda zata yanke mata hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari in har taci gaba da bata mishi suna.

ABU NA KARKE ACIKIN KOTUN

Me shari’a ya bayyana cewa Jarumar nada daman ta daukaka kara a cikin wattani uku kacal akan hukuncin daya yanke in har be mata ba.

mun gode.

hausatiktok.com

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page