Alamomi goma dake nuna cewa soyayya ta kare tsakanin ki da saurayin ki
Akwai bambanci tsakanin namiji na sonki da kuma bai sonki, wanda zai nuna hakan a aikace, a baki da kuma yanayin mu’amalar ki da shi.
Da yawan mata za su fara tunanin ko nayi wani laifi ne? Miye dalilin canzawar shi? Mi ya kamata na yi wajen kara karkato da hankalin shi a gare ni? Ire-iren wadannan tambayoyi ne da za su yi ta yawo a zuciyar budurwar da ta rasa gane kan saurayinta.
Wata ba za ta fahimci cewa sonta ne ya daina ba, sai ta fara yaudarar kanta, ta shiga halin damuwa da tashin hankali musamman idan aka yi sa’ar cewa ta mutu a soyayyar sa.
A matsayinki ta mace, wacce aka sani da rauni musamman a bangaren soyayya, ya zama wajibi ki natsu; ba’a shiga soyayya ta ka, kin san mi ki ke so game da namiji sannan ki san alamun da ke nuni da cewa wannan yaudara ce ko kuma an daina yayinki, saboda mune a mafi yawan lokutta muke fadawa ciki.
Monica Parikh dake a NYC masaniya akan zamantakewa da soyayya ta bayyana cewa matukar namiji ya fara nunawa mace halin ko in kula, babban abinda yafi dacewa da ita shine ta kama mutuncinta ta hanyar daina tirsasa cewa sai ya dawo yanda ake a baya. Idan ya bukaci ku rabu kar ki nuna hakan ya dame ki ko da kuwa a zuciyar ki ba haka bane ba. Duk wanda ya nuna baya bukatar ka, babban abinda ya dace kaima ka raba hanya da shi, babu dole a soyayya.
Idan laifi ki ka yi, abu na farko shine ya jawo hankalinki cewa kin yi kaza da kaza da basu kamata ba, ba wai ya janye soyayyar shi a gare ki ba.
Duk mai son ki da gaskiya zai so yaga canji na kwarai a tattare da ke, kuma zai taimaka wajen ganin hakan ya tabbata ba wai ya gudu a lokacin da ki ka fi bukatar kasantuwar sa a kusa da ke ba.
Mai karatu na iya duba wannan makala da ta yi tsaokaci akan dabi’ar miskilin namiji.
Mata mun fi kowa wahaltuwa a bangaren soyayya saboda mu dama komi namu da ita yake tafiya. Abu kankani ke karya mana zuciya, a lokacin daya kuma abu kankani ke dawo damu cikin walwala da annashuwa. Shiyasa komi za muyi mu kan daura shi bisa turbar so.
A wannan zamanin da mu ke ciki wanda yaudara ta yawaita a tsakanin masoya, mata da dama kan fada son maso wani.
Don haka muka ga dacewar tattaunawa a kan wannan batu domin fiddo da wadanda ke cikin ruwa daga halaka.
Alamomi goma dake nuna cewa soyayya ta kare tsakanin ki da saurayin ki
Akwai alamomin da namiji zai nuna miki wadanda ko shakka babu ya daina sonki, babu sauran burbushin soyayyar ki a cikin zuciyar sa. Amma soyayyar da kike masa tasa kina kokwanto a kan shi yana sona ko bai sona, wadannan alamomi zasu warware ma ki matsalar da kike ciki.
1. Zai yanke duk wani nau’in sadarwa dake tsakanin ku
Ma’ana duk wata hanyar da za ta hada ku kuyi magana zai datse ta, misali zai rage zuwa gidan ku fira da sunan zance. Watakila a sati da yana zuwa sau uku, daga lokacin da ya daina yin ki zai koma sau daya har sai kin wayi gari ma a sati ko keyar sa ba za ki gani ba.
Da kinyi korafi zai nuna ma ki cewa aiki ne yayi ma sa yawa.
Sannan idan ma’abocin turo da sakon text messages ne nan ma zai rage har sai ya dawo ba ki ganin ko daya.
Wajen kiran waya kowanne masoya su na da tsarin kiran junansu ta waya, wasu su kan tsara lokuttan wayar, daga lokacin da kika fahimci cewa ya daina bin wannan tsarin, kullum ke ce ke kira, bai miki bayanin komi ba to maganar soyayya babu ita.
Har ya zama duk wata magana da ta shafi soyayyar ku ke ce ke yin ta, to ki tabbatar da cewa ya daina yin ki ne. Saboda soyayya ba ta tafiya ba tare da tsimakon kowane bangare ba. Dole ne kowane bangare ya bada gudummawa.
2. Daga lokacin da ya fara kwatanta ki da wata mace
Kowace mace burinta a ce masoyinta bai da wani ido a kan wata diya mace face ita. Daga zarar namiji ya fara hada ki da wata, yana nuna gazawar ki akan wasu ababen, yana nuna miyasa ba za ki zama kamar wance ba, to ki tabbatar ya fara daina yayinki.
Duk namijin da ke sonki yana ganin kin fi kowace mace, ko da kuwa a zahiri ba haka bane ba. Ko bature ya ce “Beauty is in the eyes of beholder”.
Daga lokacin da ya fara ce miki “Mi yasa ba za ki yi koyi da rayuwar wance ba? Wai ke ba za ki koya yanayin kwalliya da adon wance ba? Ina ma a ce za ki yi iya zama mace kamar yadda wance take? Wai ke mi yasa kin cika kishin tsiya ne? Budurwar wane ba haka take ba”.
Idan ya yi mi ki haka sau daya, a lokacin kika taka masa birki na cewa ba za ki iya daukar irin wannan abubuwan ba, idan har ya cigaba alamu ne da ke nuna cewa abinda ya gani a tattare da ke ya dusashe, shiyasa har ya fara kwatanta ki da wata.
3. Daga lokacin da ya daina abubuwan da ke faranta miki rai
A matsayin ku na masoya kowane ya san abinda ke faranta ran dan uwansa. Musamman idan namiji na sonki zai yi komai dan ya faranta miki rai, zayyi abubuwan da zasu kara miki sonsa a zuciya. Babban burin shi ya samu soyayyar ki. Amma daga lokacin da bai damu da yin wadannan abubuwan ba to alamu da ke nuna cewa ya daina yayin ki.
4. Zai daina ba ki lokacin sa
Idan a da ya kan baki awa biyu ko uku a yini zai dawo ya daina kwata-kwata saboda ba ki da sauran wani muhimmanci a rayuwarsa. Zai maida lokacin sa ne akan aikinsa, karatunsa da wasu ababen da yake matukar son ganin ya cimma buri a rayuwa. Duk wadannan lokuttan da ku ka share a baya wajen ganin kun debe ma juna kewa, kuna faranta ran juna zasu zama tarihi.
5. Za ki daina birge shi
Daga lokacin da soyayya ta kare a tsakanin masoya za su daina birge juna. Dama soyayya ce ke sanya haka. A yanzu idan kika yi abinda ke birge shi a da zai dawo kina ba shi haushi. Misali a da yana son ya ga kin yi kwalliya, daga ya daina sonki, zai fara maganar kin cika kwalliya ko kuma ma bata yi miki kyau.
6. Abu kalilan za ki yi ya ga laifin ki
Wanda a da can sai dai ya gyara miki, amma daga zarar ya daina sonki, wani kalilan din abu a wajensa gagarumi laifi ne. Zai fara korafin kin yi kaza da kaza, baya son abinda kike yi. Babu maganar lallashi said ai magana cike da izza da takama.
7. Zai cire ki daga rayuwar shi
Watakila a da duk wani abu da ya shafi rayuwarsa tare kuke tattaunawa, karatun sa ne, aiki da duk wani abu da ya shafi cigaban sa, amma yanzu ba ki kara samun wannan damar. Duk wani abu da ya shafe shi zai rufe miki, har sai ya dawo tamkar bako a gare ki wanda ba ki san komi dangane da shi ba.
8. Babu wani sauran girmamawa ko kyautatawa
Duk wani girmamawa dake tsakanin ku zai dawo babu shi. Zai yi abu kan shi tsaye walau yai miki dadi ko akasin hakan, wannan ba damuwar shi bane. Zai zama “self-centered” komi ya koma a tsakanin duniyar shi ne; zai yi komi don samuwar farincikinsa.
Duk wani abu na kyautatawa ya kare a tsakaninku. Saboda babu sauran soyayyar da ta zamo bango a gare ku, yanzu ta zube.
9. Zai daina fadin yana sonki, zai daina nuna maki kulawa
Daga lokacin da soyayya ta kare a tsakanin ku, babu sauran nuna maki tsagwaron kauna da yake yi a da, koda kuwa fadin “I love you” ne masoya kan yawaita nanatawa junansu.
Duk wata kulawa da yake ba ki zai daina. Dake da babu duk daya kuke a wajen sa.
Komi na shi zai zama bakon abu a gare ki, sannan ke da sauran mutane yana maku kallon duk daya kuke. Bare har ki samu sanyi, wanda a da kullum kara jaddada soyayyarsa yake a gare ki, yana ba ki duk wata kulawa da ta kamata.
10. Damuwarki bata dame shi ba
Daga lokacin da ya juya miki baya zai fara nuna halin ko in kula, koda kuwa a lokacin da kike da damuwa ne, kika fi bukatar tausasan kalamai daga wajensa. Damuwarki taki ce ke kadai, bai ma da lokacin tsayawa ya lallashe ki. To yanzu lokaci ne da za ki sama ranki cewa soyayya a tsakanin ki da shi ta kare.
Kadan kenan daga alamomin dake nuna cewa an daina yin ki. Daga kin ga wadannan alamomi kar ki nace, ki sanyawa zuciyarki salama ki dau hakuri, sannan ki cigaba da rayuwarki.