Education

(ABU zari) Ankarya tarihin ABU zaria na shekara 60

Mufid Suleiman ya karya tarihin ABU zaria na shekaru 60 ya kammala karatunsa da 4.96 CGPA 

Mufid ABU zaria best student

 

(Ankarya tarihin ABU zaria na shekara 60) Dalibin Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Mufid Suleiman ya kafa sabon tarihi a makaranta na ABU zaria inda ya kammala karatunsa na karshe da 4.96 CGPA daga cikin 5.00 – mafi girman da aka taba samu a tarihin ABU tun bayan kafuwarta a shekarar 1962. Wanda ya yayi karatu a bangaren Noma mai lamba U16AG2026 ya ya shafe tarihin sa na baya Wanda ya gama da 4.94 cikin 5.0 .

YAYI NATIONAL DIPLOMA A SCA/DAC ABU ZARIA

Mufid ya Fara National Diploma a fannin gona a kolegin Division of Agricultural colleges, Samaru college of Agriculture, (SCA/DAC) Samaru, inda yayi karatun shi a shekaran 2005 – 2015 inda ya samu CGPA 3.69 daga cikin 4.00 CGPA Wanda anan ma shine Wanda yafi kowa daga. Ya kuma samu karramawa daga ofishin jakadanci na kasar Sin wato china da jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, a ranar 1 ga watan October na shekaran 2017, saboda tsabar kokarin daya nuna.

Mufid ya samu lambar yabo a matsayin mafi kyawun dalibi a CPPR 301 na ( Plant Disease) a shekarar 2017/2018 daga sashin amfanin gona na ABU Zaria, Karkashin jagorancin Farfesa SALLY MILLER MENTORSHIP.

Har ila yau Mufid ya samu lambar yabo ta ‘First Class Student’ daga kungiyar daliban aikin gona ta Najeriya (NASS), Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar 2018.

Mufid ya yi hidimar kungiyoyin dalibai da dama tun daga lokacin da yake karatun national diploma a SCA har zuwa matakin jami’a.

Mufid ya dauki tutorial da dama na abokan sa Wanda yake koyar dasu a Cikin aji tin daga 100 level zuwa 500 level, Mufid ya kasance beda wani lokaci na kansa saina karatun sa Kona koya ma sauran mutane karatu.

Mufid Suleiman wani mutum ne da baya son hayaniya Kuma baya fada da kowa Kuma mutum ne me son addini mufid yayi hidima da dalibai sosai wajen koya musu karatu ta inda harda Wanda suka wuce shi a aji suna koyan wasu darussa daga wajen sa ko Kuma abinda ya shafa project.

Inme karatu zai tina Nuhu Ibrahim wani dalibi daya fito daga fannin computer science na jamiar Ahmadu Bello university da 4.94 CGPA a cikin 5.00, inda ya zama dalibin dayafi kowa kwazo da samun CGPA me kyau a tarihin ABU tinda aka kafa ta.

Daga nan sai gwamnatin jihar Kaduna ta ba Nuhu Ibrahim scholarship don karantar MSc Advanced Computer Science with Specialization in Artificial Intelligence a Jami’ar Manchester.

To sai Kuma ga Mufid Suleiman ya samo CGPA da tafi na Nuhu Ibrahim shi Kuma gomnatin kaduna ne zata dauki nauyin shi ko Kuma Gomnatin Nigeria gaba daya.

Mun gode
Hausatiktok

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page