Emir of zazzau:Tsohon Wazirin Sarkin Zazzau ya kai El-Rufai da wasu mutane 13 kara kotu yana son a tsige Sarkin Zazzau
Tsohon Wazirin Sarkin Zazzau ya kai El-Rufai da wasu mutane 13 kara kotu yana son a tsige Sarkin Zazzau saboda an nada shi sarkin zazzau ba’a kan ka’ida ba. (emir of zazzau)
canza kudin nigeria shi zai hana sata inji sunusi lamido sunusi
Daya daga cikin masu zaben Sarakunan Zazzau, Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu anda yake cikin masu zaben Sarkin Zazzau na 19, ya maka Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da wasu mutane 13 a gaban Babbar Kotun Jihar, yana neman a tsige Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli. a matsayin Sarkin Zazzau.
kamar inda ya fadi an nada sarki ba’a kan ka’ida ba don sun gama zaben sarki kuma sun tura ma gwamna list din zaben da akayi amma sai ba’a yi anfani da wan nan sunaye da aka aika ba kawai sai gwamna yayi gaban kansa ya nada wanda yake so. (emir of zazzau)
gaba daya bamu tura da suna nuhu bamalli ba saboda be cika doka da ka’idoji na neman sarki amma sai gashi an nada shi a matsayin sarkin zazzau, don haka ne muke neman kotu da ta tsige shi daga matsayin sarki.