KannywoodVideos

An Kai Karan Ado gwanja gaban gwamnan Kano kan sabuwar Wakar sa ta chas asosa

Ado gwanja chas asosa

Wasu daga cikin manyan Kano harda lauyoyi masu zaman kansu sun fara fusata akan wakokin da Ado gwanja yakeyi, inda suka kaishi Kara gaban gomnan Kano da hukumar hisba, sunce Yana Bata musu tarbiyan Yara suna rawa na iskanci da wakan.

Wani lauya me zaman Kansa a garin Kano yakai Karan Ado gwanja wajen gwamnan Kano Umar ganduje.

Haka Nan wan Nan lauya me zaman Kansa ya rubuta zungureriyar wasika zuwa ga hukumar hisba da Kuma hukumar tace fina-finai.

Kamar inda wan Nan lauya me zaman Kansa ya rubuta ma wan Nan hukuma da gwamnatin Kano, yace a yanzu haka zamu zura idanu Muna kalon Ado gwanja Yana 6ata mana tarbiyan Yara a garin Kano

Wan Nan lauya yaci gaba da cewa mu Kano Muna da tarbiya na musulunci Kuma ba zamu Saka idanu Wani mawaki ya Bata mana tarbiyan yaran mu ba.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page