Kannywood

Nayi Mafarki Fati Washa Ta Rike Hannuna Mun Shiga Aljanna

Nayi Mafarki Fati Washa Ta Rike Hannuna Mun Shiga Aljanna, Inji Jarumin Kannywood Zeek-illela

Dan wasan be dade da shigowa harkar film ba a masana’antar fina-finai ta Kannywood,

Jarumin, Auwal Abdullahi Zeek Ilela ya bayyana cewa

wata rana yayi mafarkin Jaruma Fati Washa ta rike masa hannu sun shiga Aljanna.

Sabon dan wasan yace “wannan shine babban dalilinsa na shiga harkar fina-finan Hausa

saboda ya tabbatar akwai alkhairi a cikin mafarkin tunda ya hadu da Fati Washa.”

Ya kara da cewa “Na dade ina son Fati Washa domin mace ce mai kira da cikar halittar macentaka,

wata rana nayi mafarki mun hadu da ita a lahira, ga ‘yan uwana da abokaina da sauran mutane.

amma itace ta kama hannuna muka shiga gidan Ajannah tare,

Wannan dalili yasa nayu sauri na shiga cikin harkar film domin mu hadu tare tun a duniya tayadda mafarkina zai zama gaskiya a ranar lahira” Inji shi.

Dan wasan me suna Auwal Abdullahi, ya cigaba da cewa “bai san haka ‘yan film suke da kirki ba sai da ya shiga cikinsu

saboda haka mutane suke yin musu gurguwar fahimta ne a rayuwa ta zahiri amma a badili su din mutanen kirki ne,

“a daina yi wa ƴan fim mummunar fassara domin mutanen kirki ne,”. Inji

Kowa dai da abin da ya dameshi, idan kana wannan duniya ba abin da bazaka gani ba. Allah yasa mu dace ameen.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page