Kannywood

Matsallan da masu Fina-Finan Hausa suke samu a Youtube

Fina-Finan Hausa: Fina Finai Tsakanin Jiya da Yau

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

Masu Sana’ar fina-finai a Nigeria sun koma amfani da shafin yanar gizo na YouTube wajen tallata fina-finansu,

Wanda yanzun haka suke Kara Samun karbuwa Wajen Al’umma da Dama.

Wannan baya rasa nasaba da yadda zamani ya sauya,

biyo bayan samun wayoyin hannu kirar android,

Wadanda jama’a ke amfani da su a wannan zamani.

Duk da cewa masu wannan sana’ar sun dade suna kukan yadda suke tafka gagarumar asara,

Bayan sun kashe makudan kudade Wajen shirya film,

Amma wasu wadanda ake kira masu satar fasaha sai su buga fim din a fayafayen CD suna sayarwa,

Kuma akan kananan farashi ba tare da izini ba.

Masanaantar ta dade tana laluben yadda zata kawo sauyi kan wannan matsala ta satar fasaha abin ya faskara,

Duk da barazanar da sukeyi na maka wadanda suka kama da Laifin hakan.

yanzun dai kila an samu saukin satar fasahar,

Amma kuma har yanzun akwai wadanda ke sauke fina-finan daga tashar YouTube suna sayarwa ba tare da izini masu shi ba.

Sai dai hakan yasa masu Sana’ar buga hoton film din nasu suna sayarwa masu saida fina-finan,

Domin samun saukin satar fasahar da ake musu,

da kuma yadda cima zaune suke amfani da kayan da ba nasu ba.

Amma abin tambaya anan shine ko kwalliya na biyan kudin sabulu?

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page