News

‘Yan Nijeriya Kukan Dadi Suke Yi Inji Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa al’ummar kasar nan kukan dadi suke yi idan aka kwatanta irin matsi da wahalar da ake sha a ragowar kasashen Afirka.

Also Read:

Shugaban kasa: zan koma noma da kiwo inna gama Mulki

Muhammad buhari: shugaban kasa Nima kaina shinkafa yar Hausa nake ci a gida na

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a fadar Mai Martaba Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, a lokacin da ya je gabatar da addu’o’i a yau Asabar, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da Sarkin Katsina sun bayyana alhininsu kan halin kuncin da jama’a ke ciki. a karkashin mulkinsa.

Inda yake fadi da bakinsa kan cewa “Idan har mutane sun san matsin rayuwa da wasu kasashen Afirka ke ciki a halin yanzu, dole ne su gode wa Allah bisa halin da suke ciki a kasar.”

Ya kara da cewa “Don haka muna kira ga mutane da su yi hakuri, za mu iya bakin kokarinmu akan jin dadinsu a kasar.”

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya bukaci ‘yan Najeriya da suci gaba da yi wa shugaba Buhari addu’a domin gwamnatin kasa mai kabilu da addinai daban-daban kamar Najeriya na da matukar wahala.

Tuni dai shugaban ya koma babban birnin tarayya Abuja bayan kammala hutun Sallah.

Idan baku manta ba kwanakin baya ya taba cewa ‘yan nigeria zasu gane kokarin da yayi a mukinsa.

Ta wasu majiya labaran anji yace “yan Nigeria zasuce gwanda mulkinsa akan wanda zai biyu bayansa”.

Anan muka kawo muku karken wannan labarin nan. Kada ku manta da shafinmu muna kaw abubuwa da dama da ya shafi rayuwa.

Kuma muna fatan zaku dingama ‘yan uwa da abokan arziki wannan page din ta social media naku.

Mune Hausatiktok naku

Ku huta lafiya munger de sosai matuka da ziyarku wannan shafi me tattare da tarin albakarka.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page