Za’a fara azumin watan Ramadan na 2022 gobe asabar 2 ga watan april 2022 a Saudi Arabia dama sauran wasu kasashen musulmai na duniya gaba daya
Alhamdulillah kamar inda aka saba duk shekara muslumai suna azumi na wata daya wato azumin watan Ramadan wan nan wata bashi da tsayayen rana wanda ake fara shi har sai an duba wata anga wan nan jinjirin wata san nan sai a sanar kuma a wasu lokutan kasashe da yawa sukan ga wata tare su fara azumi tare wasu kasan kuma sukan fara daban kamar bayan kwana daya da farawan wasu kasashen.
zaku iya karanta: ruwan maniyi da anfanin sa
(Ramadan 2022) Wan nan shekaran ma Alhamdulillah kamar inda aka saba duk shekara akan fara duban wata daga 29 ga wata shaban in angani za’a fara azumi washe gari in kuma ba’a gani ba dole a tashi da azumi daga lokacin da watan ta cika 30 saboda watan musulunci baya wuce 30.
(ramadan 2022) To a yanzu haka gomnatin Saudi Arabia ta sanar da ganin wata kuma za’a tashi da azumi gobe asabar wato 2 ga watan april na shekaran 2022.
Kamar inda me karatu ya sani saudiya suna masu duba mata wata na musanman ta inda suka samar musu na na’ura kala daban daban domin duban watan Ramadan duk shekara
Haka nan Saudi Arabia suna ma dukkanin muslman Saudi Arabia dana duniya gaba daya barka da ganin watan Ramadan me albarka.
ga video inda akaga watan Ramadan a saudi Arabia
duk wani muslumi na fadin duniyan nan ya kamata ya tina cewa wan nan wata me albarka na ramadan wata ne da babu irinta wajen diban lada, kayi kokari kayi aikin da zaa gafarta maka a entar da kai ka ciyar da wanda basu dashi ka yawaita karatun alkurani kayi sada fiye da wanda kakeyi a baya sai ka samu ku6uta daga wuta.
Muna rokon Allah yasa muna cikin bayi wanda za’a entar guma a gafarta musu Allah ya amsa mana ibadun mu.