HealthSirrin Aure

Maganin Tsinkewar Ruwan Maniyi maza da mata

MAGANIN TSIKEWAR RUWAN MANIYI

watery sperm,maganin tsinkewar ruwan maniyi
matsalar maganin tsinkewar ruwan maniyi

(maganin Tsinkewar Ruwan Maniyi) Tsinkewar ruwan maniyi wajen maza abune da yake addaban maza saboda abune da yake hana samun haihuwa tinda yakanzo babu sinadarin haihuwan acikin sa, domin cutane ke kawo wan nan tsikear ruwan maniyi ya koma kamar ruwa.

Masana sun tabbatar da cewa tsinkewar ruwan maniyi wajen maza abu ne da yake iya faruwa ta sanadiyar cuta ko kuma halitta , wasu ma da yawa sunce ba’a haihuwan namiji a haka sai dai inya samu cutar tin yana karamin sa.

Ta inda aduk wanda ya taba ganin tsikaken ruwan maniyi kuma ya taba ganin me lafiya wanda be tsike ba zai gane akwai banbanci sosai a cikin sa ta inda zaka gane tsikaken ruwan maniyin babu sinandarin haihuwa a cikin sa don zaka ganshi ne tamkar ruwa duk da dai mun san Allah ne ke bada haihuwa, kuma haka Allah ne ya saukar da cuta kuma da maganin ta.

Amma ya kamata mu sani wani tsikewar ruwan maniyin ne me dauke da cuta ke hana ciki, amma tabbas mace na iya daukan ciki da ruwan maniyin da beda kauri wato tsinkaken ruwan maniyi ko kuma wanda zakuga yayi kauri sosai duk mace na iya daukan ciki dasu.

KADAN DAGA ABINDA KE KAWO TSINKEWAR RUWAN MANIYI

(Maganin Tsinkewar Ruwan Maniyi maza da mata) Abubuwa da dama na iya kawo sanadiyar tsinkewar ruwan maniyi kuma haka in aka nema magani akan iya dacewa a samu lafiya cikin ikon Allah, magani na asibiti kona Islamic chemist ko magani na alada wato masu maganin gargajiya, kamar inda na fada abubuwa da daman a iya janyo sanadiyar samun matsalan tsinkewar ruwan maniyi amma dai zamu dauka daya daga ciki mudanyi muku bayani akanshi wato ciwon sanyi saboda yana daya daga cikin babban abinda yake cutar da maza da mata kuma yakan iya hana haihuwa.

Kuma akiyaye istimna’I wato masturbation a turance domin wan nan abu yana daya daga cikin manyan abinda suke kasha azakarin namiji don takan hana mikewar azzakari, tana saka azzakari ta koma karama, takan saka saurin fitar maniyi, takan saka tsinkewar maniyi ya zama ruwan maniyin mutu beda kyau, kuma yakan iya kasha kwayoyin haihuwa.

Haka nan yawan saduwa da mace da yawa a rana daya kuma mutum bayacin abubuwan gina jiki yana kawo faruwan tsinkewar ruwan maniyi kuma ya koma dan kadan babu yawa, sai mutum yayi tinanin kamar beda lafiya ne, don haka yana da kyau koda mutum nacin abinci me gina jiki ya dinga daga kafa wajen saduwa da matan shi don Karin lafiya ajikin shi da matan nashi gaba daya

KADAN DAGA ABUBUWAN DA SUKE GYARA RUWAN MANIYI

Zaitul laus yana gyara ruwan maniyi sosai.

A samu albasa a yankata kanana a dama a zuba ruwa kamar kofi daya sai a dafa bayan ta dafu a sauke a tace tasha iska sai asha ayi haka kamar na sati daya.

A samu albasa da garin hulba a dafasu a tace ruwan a zuba zuma a dinga sha.

Ku a yawaita shan madara da kayan marmari da abinci masu gina jiki akoda yaushe.

Amma me karatu ya kamata ya sani cewa akwai tsinkaken maniyi da yake a hakan sa kuma lafiyarsa lau babu wani illa acikinsa kuma in aka zuba ma mace a cikin farjin ta yakan sa mace ta dauka ciki, san nan a wani lokacin idan sha’awa ta taso ma namiji ko mace zakuga wani dan farin ruwa yana fitowa saboda tsabar sha’awa duk wan nan shima lafiya ne, farin ruwan da yake fitowa haka nan wani lokacin ba tare da sha’awa ba ko kuma bayan an gama fitsari shine yake iya zama na cuta ko kuma muce ciwon sanyi na iya kawo shi ko kuma wani cutar.

Akwai wasu daga cikin mazan ko mata matsu matsalar tsinkewar ruwan maniyi ko kuma karancin ruwan maniyin ta sana diyar rashin samun isashen abinci ko kuma abinci me gida jiki wanda zai basu ruwan maniyi me yawa kuma me kyau, don haka sais u dinga tinanin ko suna fama da wata ciwo ne da zasu samu abinci sosai kuma me gina jiki ruwan maniyin su zaiyi yawa kuma zaiyi kyau ta inda da ya zuma ma uwar gida acikin jikinta zakiga tana kiba kuma jikinta na wani sheki.

Haka nan akwai fitan farin ruwa na ni’ima daga gaban mace kamar inda na fada muku a baya fitan farin ruwan kala kala ne akwai na ciwo akwai na sha’awa akwai na ni’ima wanda mace zata ga gaban ta ajike cikin danshi akoda yaushe wani ruwa na ni’ima yana jika mata pant akoda yaushe

CIWON SANYI GA MATA DA MAZA

zaku iya karanta. daren farko amarya da ango

Ciwon sanyi wani ciwo ne da yake wahalar da mata da maza musanman ma matan domin a yanzu kashi 70 cikin 100 na mata suna dauke da wan nan ciwo na sanyi wasu sun sani wasu basu sani ba, ciwon sanyi ciwo ne da ake saurin daukar sa saboda ciwo ne me yaduwa a tsakanin mutane wani na iya saka ma wani ta hanya daban daban haka nan ciwon sanyi yana da wahalar magani a jikin dan adam ta inda sai anyi da gaske ake iya samun maganin shita inda wasu ma suke ganin ba’a iya warkea daga ciwon sanyi sai dai a samu sauki na zuwa wani lokaci.

Cinwon sanyi na mata kusan shine kan gaba acutan da mata da yawa ke faa da su musanman masu aure, domin ko binciken da masana sukayi ya nuna kasha 70 cikin dari na mata suna dauke da ciwon sanyi yayin da duk yan matan aure kamar guda 10 sai ka samu 8 daga cikin su suna dauke da wan nan ciwo na sani.

Haka nan a kulum kamuwa da wan nan cuta na sanyi kara yawaita sukeyi ta inda suma maza cutaar ta kutsa zuwa jikin su musamman masu aure, kamar inda cutar na sanyi take iya illata mace ta hana ta hahuwa haka shima namiji ke faruwa dashi ya kasha mishi sinadarin haihuwa ruwan maniyin shi zai tsinke ya zama kamar ruwa babu kauri san nan zakaga gefen azzakarin namiji yana tsagewa.

KADAN DAGA HANYAR DA AKE DAUKAN CIWON SANI

(maganin Tsinkewar Ruwan Maniyi) Yawan shiga Public toilet in masu ciwon sanyi na shiga bayin, misali kamar gidan yawa ko gidan haya, ko in ana zuwa makaranta ana shiga bayin makaranta ko wajen aiki ko bayin kasuwa da sauran su.

Ga masu aure in matan ko mijin daya daga cikin sun a da ciwon sanyi to wajen kwanciyar aure daya na iya shafa ma dayan, haka nan masu yawan banza a gari karuwa kona miji me bin karuwai ana daukan ciwon sanyi sosai a nan wajen.

Anfani da kaya sama da mutum daya kamar yaya da kanwa ko yaya da kani suna anfani da wando daya wan yasa wan na tasa shima yana iya sa a dauka ciwon sanyi, ko koma masu siyan pant ko gajeran wando na gwanjo shima ana iya daukan wan nan cuta na sanyi.

zaku iya kalon video a anan: Ruwan jaraba na mata kawai

ABINDA YASA CIWON SANYI YAFI SAURIN KAMA MATA

(maganin Tsinkewar Ruwan Maniyi) Ciwon sanyi infection yafi saurin shiga jikin mace wasu matan tun suna yara suke samun shi amma be cika nuna alama ba har sai lokacin da mace ta fara alada, shi yasa yana da mihammanci iyaye mata su tabbatar suna kula da gaban yaran su mata musamman a lokacin da sukazo musu wanka, musamman in yarinyanki ta fara zuwa makaranta ko kuna gidan yawa ta shiga bayi da yarinki takeyi zata iya kamuwa da wan nan infection, shi yasa yake da mahimmanci a dinga zuba ruwa kafin a tsuguna a public toilet kafin a tsuguna.

Haka nan yana da mahimmanci ki koya ma yarinyaki yawan canza pant a rana kamar so uku  saboda aduk lokacin da mace tayi fitsari tayi tsarki to danshi ko leman a wan nan ruwan kan zauna ne ajikin pant don haka ne yake da mahimmanci ki koya ma yarinya ki karama tsafata na canza pant don kare lafiyarta.

Yawan wanke farji da ruwan sanyi Haka nan wanke farji da sabulu me kamshi ko kuma wasu daga cikin mata matsu tura yatsa a gaban su ko kuma wan abu don jin dadi akan yakan iya janyo musu ciwon sanyi me hatsarin gaske kuma me wuyan magani.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page