Sashi Daban (Others)

ABINDA YASA NA FARA RAWA DA WAKA A GIDAN GALA – TAHIR FAGGE

ABINDA YASA NA FARA RAWA DA WAKA A GIDAN GALA – TAHIR FAGGE

“Lokacin da abin ya faru, ina kwance ne a gida, ba ni da lafiya. Na samu matsalar cutar shanyewar barin jiki, har ya zama ba zan iya tafiya mai tsayi ba, a lokacin har sai na zauna na huta.

Kuma bani da kudin da zanje asibiti, kuma ina neman kudi N260,000 wanda da shi ne za a dauki hoton zuciya ta, za a dauki hoton kirjina da yi mani magani.”

Yaran nan sukazo har gida suka sameni, suka ce ko da ba zanyi rawa ba, suna so naje wajen na zauna a matsayina na babban bako.

Kuma anan taki suka dauki kudi N160,000 suka bani. Ka ga saura N100,000 kenan.

“A lokacin naga duk wanda ya fada ruwa idan aka bashi takobi zai kama, don yana neman ceto.

Da naje wajen na zauna sai masoya suka rokeni da na tashi ko tsayawa nayi a kan fulo, suka samo tsohuwar wakar da na hau tun a finafinan baya suka saka.

Sai aka rika yi mani liki, wanda kuma alhamdulillahi a wannan lokacin na samu cikon N100,000 din da nake nema da zan hada a yi mani aikin,

har ma da wasu kudin da na rike a hannu inaci da iyalina a lokacin da nake zuwa asibitin.

Amma su da su ke maganar, me su ka yi mani don ceto rayuwa ta?

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page