Sashi Daban (Others)

Cikin Watanni Uku An Haifi Yara Sama Da 27,000 A Kano

Cikin Watanni Uku An Haifi Yara Sama Da 27,000 A Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa cikin watanni uku an haifi jarirai 27,490 a fadin jihar.

Jaridar Kano wato FOCUS ta ruwaito cewa:

babban daraktan hukumar dake kula da asibitoci ta jihar Kano,

Dakta Nasiru Alhasan Kabo ne ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da shirin rarraba kayan kula da lafiya ga asibitocin kula da lafiya na matakin farko da na biyu da kuma na uku.

Doctor Nasiru ya ce kayan da aka raba da kudinsu ya kai Naira miliyan 15 na haihuwa ne da kayan bayar da na sashen kula da bayar da agajin gaggawa da na kula da yara.

Also read: Dangode Recruitment Application Form 2022/2023

Yace “a cikin adadin anyi tiyata ga mata masu ciki guda 681(CS), kuma irin magungunan da ake bayarwa suna taimakawa.”

Sannan ya jinjinawa abokan hulda saboda taimakon da suke bawa harkar lafiya a jihar.

Bugu da kari ya bukaci kungiyoyin fararen hula da su ci gaba da tallafa wa bangaren lafiya.

Cikin Watanni Uku An Haifi Yara Sama Da 27,000 A Kano

HausaTiktok

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page