Sashi Daban (Others)

Kungiyar Izala bata umurci mabiyanta akan wanda zasu zaba ba a zaben 2023 ba

Kungiyar Izala bata umurci mabiyanta akan wanda zasu zaba ba a zaben 2023 ba

Kungiyar tayi kira ga masu kir-kiran labaran karya suna yadawa da suji tsoron Allah su daina,

domin Allah yana nan a madakata yana jiran kowa.

Kungiyar Izala tace Rubutun dake yawo daga wasu jaridun karya,

masu yada labarun karya akan wai kungiyar ta umurci duk wani Dan izala ya zabi Tinubu a zaben2023,

wannan magana ba gaskiya Bane,

kungiyar izala batayi magana ga mabiyanta kan wanda zasu zaba ba kamar yadda kakakin kungiyar Ibrahim Baba Suleiman ya shaida mana ta wayar tarho.

“Dan haka duk wanda yaci karo da irin wannan rubutu yayi watsi da shi ba daga kungiyar Izala yake ba. “inji shi”

Ya kuma kara da cewa kungiyar in zatayi magana ko isar da sako ga jama’ar ta wanda ya shafi dandalin sada zumunta takan isar da wannan sako ne ta shafinta dake Facebook da Twitter wato Jibwis Nigeria.

Bincike ya tabbatar da cewa akwai wasu gungun mutane da ke zama su kir-kiri labarin karya su yada shi a kafafen sada zumunta dan cimmaAmina manufa ta su,

sun manta cewa akwai ranar da kowa zaiyi bayani akan abun da ya rubuta a wannan kafa a gaban Allah,

ranar da in ka rubutu alkhairi ko yada alkhairi, to zaka ga alkhairi, haka in sharri ka aikata ko ka yada shi,

to ka zauna da shirin ganin sharri a ranar gobe kiyama.

Kungiyar Izala bata umurci mabiyanta akan wanda zasu zaba ba a zaben 2023

Abun dake gaban mu a yanzu shine mu dukufa da addu’oi da tuba zuwa ga Allah ta’ala. Allah ya zaba mana shugabanni masu alkhairi a garemu. Amin

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page