Hausa Series

Kotu ta raba auren da kaka yayi da jikarsa tsawon shekaru 23

Kotu ta raba auren da kaka yayi da jikarsa tsawon shekaru 23

Wata babbar kotun shari’ar musulinci da ke zamanta a Tsafe dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara nan ta raba auren wani mutum mai suna Musa Tsafe da jikarsa Wasila da suka shafe shekaru 23 da yin aure.

Alkalin kotun Malam Bashir Mahe, ya yanke hukunci raba auren ne bayan sauraren karar daga bangaren masu gabatar da kara da kuma lauyoyin masu kara.

Mahe yace “auren Musa da Wasila ya sabawa koyarwar Addinin Musulunci.”

Alkalin ya kara da cewa “auren dake tsakanin ma’auratan ya sabawa Alkur’ani kamar yadda yazo a sura ta 3 aya ta 23, shafi na 79 da shafi na 77 na hukunce-hukunce.”

Ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan gazawar lauyan da ke kare wanda ake tuhuma ne.

Hukumar Hisbah ta shigar da kara ne inda take neman a raba auren na tsawon shekaru 23.

Hukumar ta shaidawa kotun cewa auren Musa da Wasila ya saba wa tsarin shari’ar Musulunci.

tace “ta tilasta shigar da kara a kan ma’auratan ne bayan kokarin da Majalisar Shawarar Musulunci SHURA da Masarautar Tsafe suka yi tun a shekarar 2020 bai haifar da ‘da mai ido ba.

Lauyan hukumar, Malam Sani Muhammed ya shaidawa kotun cewa:

“binciken da hukumomin addinin musulunci daban-daban da masarautar suka gudanar ya nuna cewa ma’auratan da sukayi aure tun wani lokaci a shekarar 1999 suna da alaka kai tsaye don haka an haramta aure a tsakaninsu.”

Muhammed yace “matakin ya sabawa koyarwar Addinin Musulunci kamar yadda aka yi nuni a cikin Alkur”ani sura ta 3 aya ta 23.”

Don haka ya roki kotu da ta gaggauta raba auren.

Musa Tsafe, yana da yara takwas tare da matarsa da aka raba aurensu.

HausaTikTok

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page