Sashi Daban (Others)

Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Wanda Ya Zagi Annabi SAW

Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Wanda Ya Zagi Annabi SAW

Kotun daukaka kara a jihar Kano ta sallami wani matashi mai suna Yahaya Sharif Aminu mai shekaru 22 da wata kotun shari’a ta yanke masa hukuncin kisa bisa zarginsa da aikata sabo.

Aminu wanda lauyansa Kola Alapini, ya wakilce shi a kotun daukaka kara,

an yanke masa hukunci ne a ranar 21 ga watan Janairu, 2021 amma ya daukaka kara kan hukuncin.

Tuni dai gwamnatin jihar Kano ta dage mayar da martani na tsawon watanni,

bayan da aka gabatar da takaitaccen bayani ga mai kara a watan Maris din shekarar da ta gabata.

Lauya Femi Falana, ya kai Gwawmnatin Kano, gaban Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Afrika kan hukuncin kisa kan mawakin Kano

Sai dai wanda ake kara bai halarci kotun ba, kuma Alapini Lauyansa, ya shaida wa kotun cewa an aika wa wadanda aka kara da sanarwar sauraran karar, amma yau bai samu halarta ba.

A hukuncin da mai shari’a Umar C.J, ya yanke, kotun shari’ar Musulunci ba ta da wani iko a kan addinin wanda ya shigar da kara, kasancewar Nijeriya. kasa ce mai bin addini.

Umar, a cikin hukuncin da ya yanke yace “Sashe na 38, na kundin tsarin mulkin 1999,

ya tanadi cewa kowane mutum na da ‘yancin yin tunani, lamiri da addini, gami da ‘yancin canza addininsa ko imaninsa.

“Wannan shine hukuncin da kotu ta yanke, an sallami wanda ya shigar da kara kuma an wanke shi,” in ji Umar.

Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke wa mawakin hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin yin sabo.

An yanke wa matashin mai shekaru 22, hukuncin ne bisa sashe na 382 (b) na kundin hukunta manyan laifuka na Kano,

na shekarar 2000, bayan an zarge shi da aikata zagin Annabi a wata waka da ya yada ta WhatsApp a watan Maris din 2020.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page