Ya Kashe Budurwarsa Akokarin Zubar Mata Da Cikin Da Yayi Mata
Ya Kashe Budurwarsa: Wani sarauyi mai shekaru 27 da haihuwa ya kashe budurwarsa mai Shekaru 13 har lahira.
Safiya Danladi, ta gamu da ajalinta ne bayan da Saurayinta Munkaila Ado ya kaita Gombe daga Bauchi domin a zubar mata da cikin daya dirka mata wanda ya kai watanni 6.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan da sukayi ram da shi.
Ado yace uwar budurwar tasa tana sane da tafiya da yarinyar da mayo domin ya zubar mata ciki.
Sai dai yace mahaifin yarinyar bai da labarin abunda ake ciki.
Da mahaifiyar yarinyar muka hada baki domin na kaita a zubar mata da ciki.
Mahaifinta bai sani ba shi yasa yake cewa ta bata. Cewar Munkaila.
Inda yaci gaba da cewa, “Na kaita garin Gombe ne a Unguwar Jeka da Fari,
gidan wata mai suna Amina Abubakar mai shekaru 50.
A nan ne matar ta baiwa Safiya wasu magunguna ta sha na zubar da cikin.
“Akan hanyarmu na zuwa kauyen Mai’ari dake Akko Local Government, sai ta soma mutsu-mutsu na ciwon ciki. Daga karshe sai ta mutu”. Ta bakin saurayin marigayiyar.
Yace bayan ta mutune da taimakon wani abokinsa suka binneta a wani lungu,
bayan da abokin nasa ya kona gawarta saboda kar a ganeta.
Tuni da ‘yan sandar jihar ta Bauchi a bisa umurnin Kwamishinanta sun cafke duk mutanen da suke da hannu a wannan ta’asar domin fuskantar hukunci.
Da fatan samari da ‘yan mata zasu ji tsoron Allah wajen yin zina bayan sunyi ciki kuma suce zasu zubar.
Allah kasa mu dace (hausatiktok)