Sashi Daban (Others)

Wani saurayi ya bukaci iyayen budurwarsa su biyashi mashin dinsa da aka sace a kofar gidan su

Wani saurayi: An yanka ta tashi

Ya bukaci iyayen budurwarsa da su biyashi mashin dinsa bayan da aka sace a kofar gidan su budurwar da ya je zance.

Wani matashi ya nemi iyayen budurwarsa da su biyashi Babur dinsa da aka sace masa yana tsaka da yin zance da budurwar tasa a falon gidan su.

Bayan kammala zance ya fito waje da niyyar ya dauki Babur din nasa wanda ya ajiye a kofar gidan su Budurwa tasa sai dai yaga fili babu Mashin babu alamar sa.

Dama dai idan yazo zance falon cikin gidan su Budurwar take kaishi don yin zance.

A fusace matashin yake fadin cewar gaskiya shi ba zai yadda ba ko dai a fito masa da Mashin din sa ko kuma a Siya masa sabo amma shi ba zai tashi daga kofar gidan ba, Kuma ba zai dauki asara ba.

Rahotan ya baukaci a boye sunan inda abun ya faru, sai dai idan dama ta bayar zaa iya bayyanawa nan gaba.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page