Sashi Daban (Others)

Ku Hana Matanku Da Yaranku Kallon Finafinan Hausa Domin Bala’i Ne

Ku Hana Matanku Da Yaranku Kallon Finafinan Hausa Domin Bala’i Ne, Cewar Shaikh Bello Yabo

Malamin addininKannywood,

i a jihar Sakkwato Shaikh Bello Yabo ya soki lamirin masu shirya fina-finan hausa yana cewa ‘bata tarbiya suke yi.

Malam Yabo wanda ya yi fice wajen gwagwarmayar addini da goya wa gaskiya baya,

ya bukaci iyaye da su hana yaransu da matansu kallon fina-finai,

“domin babu alkhairi a cikinsu ko kadan” a cewarsa.

Ya kuma ambaci sunayen wasu jaruman Kannywood,

wanda suka hada da Ali Nuhu, Adam Zango, Ado Gwanja, Sani Danja, Rahama Sadau da Fati Washa.

ya bayyana su cewa tambad’addu ne lalatattu kuma fasikan musulmi wanda a karan kansu ma ba tarbiya ce da su ba balle har su iya baiwa wani.

Baban Asma’u Malam Yabo ya ce

“Su kansu ba su da tarbiyya lalatattun mutane ne. Larabawa na cewa

“فاقد الشيئ لم يعطه” wato “wanda ba shi da abu ba zai iya bayar da shi ba”

Adam Zango ya goya Rahama Sadau ba aure a tsakaninsu ita ce tarbiyar da za a koyar?

Kuna can wajen wa’azi matarka na kallon su Ado Gwanja a gida,

matarka ba kai take tunani ba Ali Nuhu take tunani.

Don haka ku hana shigar fim cikin gidajenku da na Hausa da na #Turawa.”

Bayan Shaikh Yabo, da yawan malaman addinin musulunci na yin Allah wadai da masu shirya fina-finan Kannywood,

dogaronsu shi ne suna ‘bata tarbiya ta hanyar kalaman batsa, da shigar tsiraici da sauransu.

Duk da cewa gwamnatin Kano ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje karkashinta akwai hukumar tace fina-finai da dab’i a jihar Kano,

wacce ta gaza magance batsa, shigar tsiraici da lalatar da ake nunawa a finafinan hausa.

Masu sharhi na ganin tamkar gwamnati na barnatar da kudinta a banza ne,

domin babu wani aiki da hukumar ke yi wajen magance badalar da akeyi a fina-finan Kannywood.

Ko a kwanakin nan an sami wani shaidanin Yaro mai suna 442 yana wakar batsa da alfahasha,

kuma yana shigowa Kano ya yi harkokinsa amma hukumar tace finafinai ta kasa d’aukar matakin a kansa,

wanda dalilin haka ne aka samar da hukumar.

Malaman addinin musulunci na yawan caccakar gwamnatin Kano kan kyale masu lalata tarbiyya suna cin karansu babu babbaka lamarin da suka ambace shi cewa rashin kishin addini ne.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page