News

Nasiru El-rufa’i ya rantse zai kore duk malaman da suke yajin aiki na ASUU

Nasiru El-rufa’i ya rantse zai kore duk malaman da suke yajin aiki na ASUU

Gomnan Kaduna malam nasiru Elrufa’i yayi rantsuwa da Allah zai kora dukkanin malaman jami’a na KASU da suke yajin aiki.

Saboda jami’a na KASU ba suna karkashin gomnatin tarayya bane suna karkashin gomnatin jaha ne

don haka bega dalilin da zaisa suyi ta yajin aiki tare dasu ba.

Also Read: Anrufe wata babbar university a Abuja saboda rashin tsaro

Yan Nigeria Kukan Dadi Sukeyi Inji Buhari

Don haka dole malaman jami’a na KASU su koma bakin aikin su

in Kuma ba haka ba yayi rantsuwa da duka zai Kore su yayi sabon daukan aiki.

Elrufa’i ya Kara da cewa a baya sunyi irin wan Nan ya daga musu kafa,

amma yanzu bazai yarda ba dole su koma aiki ko Kuma su fuskanta fushin gomnatin Kaduna.

A baya Nasha suna zuwa aikin su ne yasa nace aci gaba da Basu albashi,

amma a yanzu tinda na Gane basa zuwa aiki to dole ne su dawo da duk kudaden da muka biya su na albashi tinda basa zuwa aiki.

Nasiru El-rufa’i yaci gaba da cewa dole ne su dawo ma gwamnati da kudin su

tinda gwamnatin tarayya tayi umurni da duk Wanda beyi aiki ba kada a biya shi Albashi.

A yanzu haka mun nada wasu daga jikin manyan gwamnatin Kaduna don yin bincike akan jami’a ta KASU

da Wanda suke aiki da Wanda basa zuwa aiki domin daukar matakin Daya kamata akan kowa.

Gomanan Kaduna nasiru Elrufa’i yakara da cewa ba zamu Saka idanu ba Muna ganin za’a kashe mana makaranta Kuma mu Saka idanu mu kyale zamu dauka mataki.

Zamu sallame su gaba daya mu Saka tallan daukan sabbin malamai a gidajen jaridu.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page