News

Za’a karawa ‘yan Najeriya kudin amfani da waya

Za a kara wa ‘yan Najeriya kudin amfani da waya nan da wani dan lokaci,

bayan da gwamnatin kasar ke shirin sanya wani sabon haraji kan kamfanonin sadarwa.

Hakan ya biyo bayan bayanin da Ministar Kudi da Kasafi da kuma Tsare-tsaren Kasa Zainab Ahmed,

tayi ne cewa gwamnatin tarayya zata dorawa kamfanonin sadarwa biyan harajin kwastan na kashi biyar cikin dari.

Ministar tayi bayanin ne a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tsarin harajin kwastan dinne,

A jiya Alhamis a Abuja, wanda hukumar sadarwa ta kasar (NCC) ta shirya.

Also Read: ‘Yan Bindiga: Zamu Sace BUHARI Da El-Rufai A Wani Sabon Bidiyo

Mora garabasan free browsing da Glo naka

Kasancewar daman tuni masu amfani da waya suna biyan kashi 7.5 cikin dari na harajin kayan alatu (VAT),

a yanzu wannan harajin na kwastan na kashi 5 cikin darin ma zai hau kan masu amfani da wayar ne.

Nawin zai hau kan masu amfani da waya ne kamar yadda shugaban kungiyar masu kamfanonin sadarwa a Najeriyar (Association of Licensed Telecom Owners of Nigeria (ALTON)), Gbenga Adebayo ya sanar.

Mista Gbenga yace kasancewar bazasu iya saukaka kudin amfani da waya da sauran hanyoyin sadarwar ba,

wannan ne ya sa dole su karkatar da nauyin ga jama’a.

Yacee zasuyi hakan ne saboda “Tuni daman suna biyan haraji-haraji har 39,

ga kuma matsalar wuta da suke fama da ita inda suke kashe makudan kudade wajen sayen man gas na dizil.”

To ‘yan Najeriya kufa kunji, Allah ya Kawo mana sauki a kasanmu.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page