Life Style

Jaruma Hauwa Waraka: Ina Neman mijin aure bazawari ba saurayi ba

Jaruma Hauwa waraka: Ina Neman mijin aure bazawari ba saurayi ba

A wata hira da BBC tayi da Jaruma hauwa waraka acikin Shirin daga bakin me ita,

inda sukayi mata tambayoyi dayawa kamar su sunanta, garinta, yarenta da inda akayi tashiga cikin harkan film.

“Da yawan mutane suna min kalon karuwa yar iska yar shaye-shaye”.

Wanda Kuma a zahiri ba Hakan nake ba yanayi ne kawai na film,

saboda fadakar da mutane yasa nake fitowa a Hakan dukda nasan ba Hali bane me kyau.

Also Read: Zamu fara kama masu canjin kudi a Nigeria – CBN

The Pressure of Life: Nigerians Are Crying Sweetly – Buhari

Irin Kallon Da Ake Mana

Da yawan mutane suna ma Yan film gaba dayanmu ba mutanen kirki bane Yan iska,

ta inda harda su suke raba Aljanna da wuta to ba zasu kaimu Aljanna ba wuta zasu jefa mu,

Kuma Hakan ba adalci bane.

Hauwa waraka ta Kara da cewa “nasani ko Ina akwai mutanen kirki akwai na banza,

amma duk film din da muke shiryawa muna yinsa ne domin fadakar da mutane da Kuma nishadi.”

Asalim Fayanan Jarumar

Asalin sunanta hauwa Abubakar anma anfi sanin ta da hauwa waraka,

Tin Wani film da tayi me suna waraka daga Nan ta samo sunan hauwa waraka.

Hauwa waraka yar asalin garin Jos ne amma ta girma a garin Kano,

inda ta fara wasu film kanana Wanda ba kowa yasansu ba,

inda a lokacin bani nake fitowa a jarumar film dinba karani kawai akeyi.

Hauwa waraka taci gaba da cewa a yanzu haka bani da aure Kuma Ina Neman mijin aure,

amma ba saurayi ba bazawari nake nema Wanda yake da hankalin kanshi yasan darajan aure Kuma zai iya rike mace.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page