Life Style

Labarina: ummee alaqa zata canza nafisa Abdullahi a Shirin labarina

Jaruma ummee alaqa zata maye gurbin jaruma nafisa Abdullahi a cikin Shiri me dogon zango na labarina Wanda ake sa ran za’a ci gaba da gabatarwa Nan Bada dadewa ba.

Shirin film na labarina Shiri ne me dogon zango Kuma Shiri ne me farin jini da mabiya da yawa inda ya samu shiga da farin jini sosai cikin kasa Nigeria har dama kasashen ketare film ne Wanda ya shahara sosai wajen nuna soyayya da kiyayya da yaudara harma da cin Amana.

A ranar lahadin da ta gabata ne jaruma ummee alaqa ta wallafa a shafin ta na Instagram hoton ta da hoton jaruma nafisa Abdullahi inda ta rubuta ma mabiyan ta tana tambayan su “Wani rawa kuke ganin zan taka a matsayin nafisa Abdullahi acikin Shirin film na labarina”

Hakan ya kawo Cece kuce da yawa acikin shafin nata na Instagram inda wasu suke fadan magana me Dadi wasu Kuma akasin Hakan.

Saurayi ya Maka hadiza Gabon a kotu saboda taci mishi kudi taki auren shi

In me karatu be manta ba a lokacin da ake tsaka da tsiya a tsakanin nafisa Abdullahi da naziru sarkin waka, babban cinedu yayi wata magana kamar haka “abinda yake kawo rigima a tsakanin jaruman Shirin labarina da me film din shine baya biyan su inda ya kamata”

Amma ita Kuma nafisa Abdullahi ta fitar da wata doguwar wasika inda take cewa ba Wani Abu bane yasa nabar Shirin labarina sai don wasu mahimman ayyuka da suka taso min Wanda bazai yuwu na hadasu ayyukan nawa da kasancewa na a jaruma acikin Shirin na labarina, asana diyar Hakan zan dakata da fitowa acikin Shirin na labarina.

Ummee alaqa zata canza nafisa Abdullahi
Ummee alaqa zata canza nafisa Abdullahi acikin Shirin film na labarina

To har yanzu dai malam aminu Saira be fito yace komai ba agame da wan Nan magana da yake ta karade shafikan sada zumunta, amma dai Muna Jira Muji ta bakin shi.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page