Hausa News

labaran duniya na yau da hausa

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Dakin Kwanan Dalibai Mata a Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da 2

'Yan bindiga sun sace daliban jami'a guda biyu a Zamfara

 

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da sace wasu ‘yan mata daliban jami’ar tarayya da ke Gusau
  • An ruwaito cewa, ‘yan ta’addan sun kutsa har cikin dakin kwanan dalibai, inda suka yi awon gaba dasu
  • Ya zuwa yanzu, jami’ai na ci gaba da aiki don tabbatar da sun ceto ‘yan matan da kuma kame ‘yan ta’addan

Bungudu, jihar Zamfara – Wasu tsagerun ‘yan bundiga sun sace dalibai mata biyu na jami’ar tarayya da ke Gusau (FUGUS) a jihar Zamfara.

An ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi 2 Afirilu, 2023 lokacin da ‘yan ta’addan suka farmaki dakin kwanan daliban da ke Sabon-Gida.

Sabon-Gida dai wani kauye ne da ke kusa da babban kofar jami’ar, kuma ‘yan ta’addan sun daure masu gadin gidan daliban ne kafin aikata barnar satar.

 

Muna Alfahari Da Ke”: Dattijuwa Ta Samu Fiye Da Miliyan N44 Bayan Bidiyonta Ya Yadu

Dattijuwa zaune cikin bakin ciki da kuma ita tsaye da wani

 

  • Wata ma’aikaciya mai suna Nola ta samu tallafin zunzurutun kudi har fiye da dala 100,000
  • Hakan ya kasance ne bayan an gano matar a cikin wani bidiyo da ya yadu a TikTYok zaune ita kadai cikin bakin ciki
  • Masu amfani da soshiyal midiya da suka ci karo da bidiyon a TikTok sun taimaka mata kuma zuwa yanzu sun tara mata fiye da $100,000

Wata ma’aikaciyar kamfanin Walmart, Nola, ta samu dalilin sake farin ciki a rayuwarta bayan ta samu kyautar kudi fiye da $100,000 (miliyan N44.3) daga wasu bayin Allah.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano dattijuwar matar zaune ita kadai a dakin hutu na Walmart, kuma hakan ya sa masoya tausaya mata.

Mai amfani da TikTok Dbon973_ ya wallafa bidiyon mai tsuma zuciya a dandalin dauke da taken:

Tuni bidiyon ya yadu kuma an bude mata asusun GoFundMe don samun tallafi daga manyan mutane. Cikin awanni 24, an tara mata fiye da $100,000.

Dbon973_ ya kuma wallafa bidiyo mai tsuma zuciya inda ya hadu da Nola domin tura mata kudin jim kadan bayan nan.

 

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

 

  • Wani bidiyo na jarumar Nollywood, Mercy Aigbe tana mai sake gabatar da kanta a sabon addininta ya yadu
  • An yi hira da ita ne a wani taron Ramadan da jarumar ta shirya tare da mijinta wanda ya samu halartan manyan jarumai
  • Bidiyon wanda tuni ya yadu ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya

Mercy Aigbe ta sa masu amfani da soshiyal midiya yamutsa gashin baki bayan bayyanan wani bidiyonta da ya yadu.

Ku tuna cewa jarumar da mijinta, Adekaz sun gayyaci abokai, abokan sana’a da yan uwa zuwa taron Ramadan.

Bayan nasarar da ta samu a taron, an yi hira da jarumar inda ta tabbatar da cewar ta bar addinin kirista zuwa na Musulunci.

A bidiyon, an iya gano jarumar tana sake gabatar da kanta da sunayenta da suka hada da na Musulunci.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page