Daren farko na lura nonuwanta na bogi ne ba manya bane
Daren farko na lura nonuwanta na bogi ne, ba manya ba ne – Miji ya kai kara kotu
Ikon Allah, kowa dai da abin da ya damesa.
Wani magidanci ya kai matarsa kotu bisa laifin damfara ta hanyar amfani da rigar da ke kara tsayin nonuwanta kafin ya aure ta.
Mista Elmiea Akdenduwa, ya kalubalanci matarsa Pyria a gaban wata kotu a California, kuma nan take ya bukaci a raba aurensu.
A gaskiya ni mutum ne mai son manyan nono, kuma na fi gamsuwa a lokacin da nake bukata,
sai dai lokacin da tazo gidana da daddare na fara ganinsu kanana a zahirance, wanda hakan bai sani farin ciki ba.
“Yanzu na fahimci rigar ciko take sawa, kuma bazan yarda da haka ba,
Na kashe kudi da yawa amma ban biya bukatata ba.
Ya kamata a raba aurennan, kuma a biya ni kudin da na kashe a kanta” inji shi.
Pyria ta ce, “Abin da yake fada ba gaskiya ba ne, ya kan taba duk sanda ya zo wurina. Na san halinsa yakan bi mata.”
Ta kara da cewa
“An gaya min cewa kar na kuskura na aure shi,
domin ya auri mata akalla 10 kuma ya sake su duka ba tare da sun aikata laifin komai ba.”
Alkaliyar kotun ta ‘dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Satumba na shekarar dubu da ashirin da biyu.
Kar dai ku manta ku cigaba da ziyartan shafinmu domin cigaba da sauraren wannan ‘karan.
Mun gode