Ya aureta lokacin da mutane ke gudunta, har sun sama karuwa
Ya aureta lokacin da mutane ke gudunta, Allah ya azurta su da samun karuwa
Hakika wadannan bayin Allah sun burgeni matuka,
Musamman matashin da yayi jarunta ya auri matashiyar wacce fuskarta ta canza sakamakon kunar wuta.
Jama’a wannan shine soyayya na gaskiya,
kyawun fuska ina daukarsa yaudara ne,
domin kyan fuska wani abune kawai da yake gamsar da bukatar kwayar idanuwa.
Samari da ‘yan mata watakila ba zasu fahimci wannan zancen nawa ba a yanzu,
amma duk wanda yayi aure ya haihu da matarsa haihuwa daya biyu zuwa uku zaifi kowa fahimtar abinda nake nufi cewa:
kyawun fuska yaudara ne kawai, bukatar ido yake gamsarwa.
Muna rokon Allah Ya kara musu aminci da yalwar arziki a cikin aurensu,
Allah Ya raya abinda suka samu, Yasa su amfana duniya da lahira.