News

Bankin Zenith Ya Rufe Dukkan Reshen Kasar Nan Cikin Karancin Naira

‘Yan Najeriya da ke amfani da bankin Zenith sun mamaye kafafen sada zumunta daban-daban don kokawa kan rashin ayyukan yi ta yanar gizo da ake fama da su a yayin da karancin kudin da aka sake fasalin ke kara ta’azzara.

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da aka rufe rassan bankin da ke fadin kasar ga kwastomomi.

Yawancin abokan ciniki na bankin sun ba da rahoton ziyartar rassan bankin kawai don gano kofofin a kulle.

ZENITH BANK

“Saboda rashin tsaro, ba mu bude yau ba,” wani jami’in bankin ya shaida wa daya daga cikin wakilanmu.

Tun bayan zuwan wayoyin komai da ruwanka, da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun mayar da tsarin banki na wayar hannu da suka fi so a kan layi don yin hada-hadar kudi.

Wasu abokan huldar bankin Zenith sun yi amfani da shafin Twitter suna kiran cibiyar hada-hadar kudi.

A ranar Litinin ne wani faifan bidiyo ya bayyana a yanar gizo, wanda ake zargin wasu ma’aikatan bankin Zenith ne da ke zare shingen don tserewa daga harabar bankin sakamakon matsin lamba daga abokan hulda.

A ƙasa akwai wasu martanin Twitter:

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page