Hausa News

Wani Mutum Ya Rataye Kansa Saboda Budurwarsa Tayi Aure

Wani Mutum Ya Rataye Kansa Saboda Budurwarsa Tayi Aure

TSANANIN SO: An tsinci gawar wani mutum da ya rataye kansa saboda budurwarsa ta yi aure a Jigawa

Hukumar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tsinci gawar wani mutum da ya rataye kansa a jikin itace saboda budurwarsa da yake tsananin so ta auri wani.

‘Yan sanda sun tsinci gawar wannan mutum ne a kauyen Kanti dake karamar hukumar Kazaure.

Mazauna kauyen basu gane ko wanene shi ba amma dai an tsinci wani katin aure a cikin aljihunsa.

Kakakin rundunar Lawan Adam ya bayyan cewa sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa sunan mutumin Ibrahim Adamu Mohammed mai shekaru 42.

Adamu ya ce Mohammed mazaunin garin Kano ne.

‘Yan uwan mutumin daga Kano sun bayyana cewa mamacin ya kashe kansa bayan ya samu katin gayyatar auren budurwarsa dake jihar Jigawa.

Bayan ya gano gaskiyar lamarin sai ya kashe kansa ta rataya a jihar.

Zuwa yanzu gawar mutumin na ajiye a dakin ajiyan gawa dake asibitin Kazaure.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page