Hausa News

Wata Budurwa Ta Gudu Da Motar Saurayinta Bayan Yaje Saya Mata Shawarma

Wata Budurwa Ta Gudu Da Motar Saurayinta Bayan Yaje Saya Mata Shawarma A Jihar Kano

Hukumar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata budurwa mai suna Ilham Kabir Karaye da ake zarginta da sace motar saurayinta bayan da ya fita sayo mata Shawarma a unguwar Kofar Famfo da ke kan titin Jami’ar Bayero.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai.

A cewarsa sun samu rahoto daga wajen wanda aka daukewa motar ne,

inda ya kai korafin cewa an sace masa mota.

Bayan da ‘yan sandan suka kama budurwar Ilham,

ta bayyana cewa tanabin saurayin nata kudi ne har naira N150,000 kuma tana ganin ba zai bata ba hakan yasa ta yanke shawarar dauke masa mota.

Sai dai a cewar saurayin, sun yi waya ne kuma suka hadu a hauren wanki,

inda daga nan tace tana jin yunwa kuma shawarma take son taci,

sai dai fitarsa ke da wuya domin siyo mata ya dawo ya tarar da motar ta yi batan-dabo.

Ilham dai ta bayyana wa ‘yan sanda cewa wani saurayinta ta kirawo ya tuka motar ya tafi da ita gida ya ajiye mata kuma ta dauki motar ne domin kudin da take bin sa.

Tuni dai aka kama Ilham da saurayin nata da ya tuka motar domin ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page