Hausa News

Wani matashi dan shekaru 20 ya yiwa matar ubangidansa fyade

Wani matashi dan shekaru 20 ya yiwa matar ubangidansa fyade a jihar Katsina

Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Jume Bello da laifin yiwa matar ubangidansa da wasu mata biyu fyade a kauyen Jikamshi da ke karamar hukumar Musawa.

Da yake gabatar da wanda yayi fyaden tare da wasu masu laifin a gaban manema labarai a ranar Alhamis,

jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP Gambo Isah,

yace “wanda ake zargin bayan ya samu nasarar aikata mummunar aika-aika ” Zina” da matan, ya kuma sace musu kudi da sauran kayayyaki.”

SP Gambo Isa ya kuma kara da cewa, “a ranar 31 ga Mayu, 2022, da misalin karfe 9:00 na dare, wadanda abin ya shafa ‘yan shekara 18 zuwa 25,

dukkansu a kauyen Jikamshi, sun kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na Musawa cewa a ranaku da lokaci daban-daban,

wani Jume Bello mai shekaru 20 da abokan aikinsa sun shiga gidajensu sun kai musu hari da wuka,

Sukayi musu barazana inda suka kwace masu abubuwanda da suka hada da kudadensu, wayar hannu, da kuma tilasta musu suka keta masu haddi.

Wanda ake zargin ya shaidawa manema labarai cewa, “a ranar ne maigidana ya umarce da in kirawa matarsa mai sayar da ruwa,

bayan na dawo da yamma ne na aikata mata wannan mummunar aika-aika.”

Ya kuma da cewa “Eh, tabbas na karbe mata ‘yan kudadenta, dana sauran jama’a.

Nayi amfani da wuka ne don tsoratar da su. Na kai daya daga cikinsu a bayan gida nayi zina da ita yayin da nayi da ragowar matan akan gadon aurensu.”

A wani labarin makamancin wannan, rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wani da ake zargin dan kungiyar ‘yan banga ne da laifin fashi da makami.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan ta jihar Katsina,

Wato CP Gambo Isah yace ” da misalin karfe 11:30 na dare, rundunar ‘yan sandan ta samu nasarar cafke wani Usman Haruna mai shekaru 23 a kauyen Ruwan Godiya,

wanda ake zargin dan fashi da makami ne.”

A binciken da akeyi an gano cewa wanda ake zargin ya hada baki da wasu mutane uku, Nasiru Ali, Adamu, da Sa’adu.

mazauna kauyen Rowan Godiya ne, sun kai hari tare da yin garkuwa da wani direban babur mai suna Ibrahim a jihar Nasarawa.

Sun yi masa munanan raunuka wanda yayi sanadin mutuwarsa,

suka tafi da babur dinsa zuwa kauyen Ruwan Godiya inda aka kama wanda ake zargin sannan aka samu nasarar gano babur din.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page