Sai Na Baiwa Matata Makudan Kudade Take Ba Ni Kanta
Sai Na Baiwa Matata Makudan Kudade Take Ba Ni Kanta inji wani magidanci
Wani magidanci ya nemi kotu ta raba aurensu saboda matarsa tana tatsar makudan kudade kafin ta amince yayi mu’amalar auratayya da ita.
Babbar Kotun Jihar Kwarra ta raba auren, bayan sun shekara 28 da matarsa.
wanda yake zargi da yawan kwartanci na wuce hankali.
Magidancin ya shaida wa kotun cewa matar,
“Takan shardanta mini da inbata cekin kudade masu tsoka kafin ta yarda in kusance ta,
idan ban ba ta ba kuma bazata amince ba kwata-kwata.”
Ya shaidawa kotun cewa: kwartoncin matarsa ya wuce misali,
domin kwartayen nata na da yawa, kuma har ‘ya’yanta take turawa karbar kudi daga wurinsu.
Har kwashe kayanta tayi daga uwar dakanmu taje ta tare a dakin saukar baki.
Ni kuma bata yarda in kusanceta sai idan na bata cekin makudan kudade,
idan naki kuma sai dai in hakura,” kamar yadda ya shaidawa kotu.
Yace tsabar rashin kamun matar tasa yasa tayi watsi da nauyin da ke kanta a matsayin matar aure.
“Aurenmu ya riga ya rushe tunda har takai ga ni da ita ba ma iya zama mu tattauna abin da ya shafi rayuwarmu da ‘ya’yanmu”, injishi.
Lauyan mijin, Mista Josiah Adebayo, ya gabatarwa kotun hoton tsiraicin matar tare da saurayinta da aka samu a cikin wayarta a matsayin shaida.
Don haka mijin ya bukaci kotu ta raba auren amma tabashi damar kula da ‘ya’yan dake tsakaninsu.
Amma martaninta, Roseline ta musanta tuhumar da ake mata,
sannan ta zargi mijinta da bin matan banza.
Ta bayyana cewa, bata kalubalantar bukatar mijin nata da kotu ta raba auren,
amma tana so kotu ta mallaka mata wani bangare na gidansu da suke zama a Legas.
A cewarta, ita da mijin ne suka yi hadaka wajen gina gidan.
Alkalin kotun, Mai Shari’a S.T Abdulqadri, ta amince da bukatar mijin,
tana mai cewa ta gamsu da shaidar da aka gabatar dake tabbatar da zargin da akeyi akan matar tasa.
Ta kuma karyata ikirarin matar na hakki a gidansu na Legas, da take so a mallaka mata wani bangarensa.
Amma kotun bata bawa kowanne daga cikinsu hakkin riki yaran ba,
saboda sun mallaki hankalin kansu, kowannensu yafi shekara 20 da haihuwa.