Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 10, Ta Raba Wasu 2,538 Da Muhallansu
Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 10, Ta Raba Wasu 2,538 Da Muhallansu A Adamawa
Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da rasuwar mutum goma sakamakon ambaliyar ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar.
Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (ADSEMA), Dokta Sulaiman Muhammad ne ya bayyana hakan ranar Lahadi.
Ya kuma ce suna kokarin gano gawarwaki uku daga wancan adadi,
yayin da sauran ukun da suka ceto kuma aka sallamo su daga asibiti.
Har ila yau, Shugaban hukumar ya ce yanzu jihar na da jimillar mutum 2,538 da suka rasa muhallansu.
Rahotanni dai na nuna yadda tafkuna a kauyukan karamar hukumar Girei da dama ne suka yi ambaliya, tare da lalata gonaki da gidaje.
Doctor Sulaiman ya kuma ce hukumar za ta fara raba kayan tallafi ga yankunan da lamarin ya shafa nan ba da jimawa ba.