Wani mutum ya kashe Naira 5.6m don ya koma kare
Wani mutum ya kashe Naira 5.6m don ya koma kare
Mutane sun dinga kiran wani mutum da mai wauta akan yadda ya kashe kudin pounds 12,500,
Wanda ya yi daidai da Naira Miliyan 5 da dubu dari Shida, don ya koma kare.
Mutumin dan asalin kasar Japan ne kuma ya je har Tokyo don ya mayar da kansa kare da taimakon masu hada kayan.
An kai masa kayan kare a watan da ya gabata inda ya dinga yada bidiyonsa sanye da kayan karen ya na rawar wakar karnuka.
Bidiyon nasa sun nuna yanda ya dinga juyi a kasa kuma yana amsa umarni tamkar kare.
A bidiyonsa na farko ya bayyana cewa:
“Na zama collie ne saboda ina son komawa dabba.
Amma yanzu inata tunanin yada bidiyona”, a cewarsa.
Kamar yanda labarun Japanese suka nuna, ya kashe kudin pounds 12,500,
inda ya siya kayan karnukan daga Zeppet wanda ya ke shirya kayan dabbobi don fina-finai.
Bidiyoyin nasa sun janyo surutai daga mutane da dama.
Yayin da wasu suka dinga yaba masa, wasu kuma sunga wautarsa.
“Kalli wata sakarar hanyar kashe kudi!
Amma yayi kamar karen gaske, kamar kyakkyawan kare.” kamar yadda wani ya yi tsokaci.
“Wannan kuma cewa yayi “ai wauta ce.”
Idan kana duniya baka rasa abin kallo. Allah dai ya kara tsaremu da tsarewansa. Ameen!