Kasashen Da Suka Fi Sauran Kasashen Duniya Yawan Karuwai
Kasashen Da Sukafi Karuwai: Duk namiji ko macen da za’ayi zina da ita ko dashi saboda a biyasu kudin wadannan sune ake kira karuwai.
A duk duniya babu kasar da basu da irin wadannan mutanen masu sana’ar karuwanci musamman ma mata.
Duk kuwa da ana samun mazan da mata suke biyansu suyi zina dasu, da kuma mazan da maza suke biya suyi luwadi dasu.
Akwai wasu kasashen guda goma da suka shahara wajen yawan matan da sukafi sauran kasashen duniya yawan mata karuwai. (Kasashen Da Sukafi Karuwai)
Wadannan kasashen sun hada da:
Na Daya
Thailand: Rahotannin sun tabbatar da cewa kasar tana daga cikin jerin kasashen duniya da karuwanci ya zama ruwan dare.
Duk wani bakon daya taba zuwa babbban birnin Kasar wato Bangkok, yasa wata unguwar da ake kira Red light.
Anguwace guda zalla babu macen arziki a nan idan banda karuwai, ‘yan daudu da gidajen rawa.
Wannan yasa aka tabbatar da kasar itace lamba daya mai tarin karuwa a duniya.
Na Biyu
Cambodia: Duk da irin hukunci mai tsauri da gwamnatin kasar ta saka ga duk macen da aka kama tana karuwanci.
Babu abun da yakai mace karuwa saukin samu a kasar ta Cambodia.
Babu kasar data kai kasar kananan matan da basu kai shekaru 15 ba karuwanci.
Haka ma iyayen ‘ya’ya mata sukan sayarwa mai bukata yarsu idan yana so a kaita gidansa ya maidata sadakarsa.
Saboda yadda mazan nasu ke son yin zina da mace budurwa, hakan yasa wasu iyayen suke sayarwa maza masu bukata.
Karuwanci mata na kasar dai ya shaharan da har yana yiwa kasar illa.
Na Uku
Neitherlands: Wannan kasar karuwanci halas ne musamman idan mace ta yanki tikitin yin sana’ar daga wajen gwamnati.
Farashin karuwai yana kamawa ne daga euro 30 zuwa 100, suma suna da Jan Layi wato Red light.
Inda zaka rika ganin mata karuwai tsirara a cikin glass ana tallansu kamar yadda kasan ana tallan meat pies acikin glashi.
Na Hudu
Colombia: Bayan shaharan da kasar tayi a duniya akan fataucin muggan kwayoyi,
bincike kuma ya kara ganowa kasar itace ta 4 a duniya da mata suke karuwanci.
Bayan halatta sana’ar karuwanci da kasar tayi. Tana da kuma doka mai tsauri na hukunta duk wata karuwa da bata zuwa ganin likita duk wata domin a tabbatar da lafiyarta, dokar da karuwan kasar suke binsa sau da kafa.
Na Biyar
Dominican Republic: Gata karamar kasa a tsubiri, ga rashin mutane da yawa a kasar,
amma sai da suka zama na 5 a harkar karuwanci a duniya.
Hakan kuwa ya farune yadda matan makotar kasar musamman Haiti da suke shigowa ba bisa ka’ida ba, sune suka cika kasar da harkar karuwanci.
Biranen su biyu da ‘yan yawon shakatawa suka fi ziyarta,
anfi samun yawan karuwai saboda rashin abunyi a yankunan ga kuma baki ‘yan yawon bude ido da shakatawa suna shigowa a kullum.
Hakan yasa suka zabi karuwanci domin raba kansu daga talauci.
Na Shiga
Philippines: Nanma dai gwamnatin kasar ta hana sana’ar karuwanci.
Kuma akwai tsanani hukunci akan duk wacce aka kama tanayi.
Turawan Yamma ‘yan kasuwa da kuma na gabashin Asiya da suke zuwa kasar kasuwanci suke lalata matar kasar da nemansu domin kwantar musu da sha’awar su.
Na Bakwai
Kenya: Ba abun mamaki bane idan mai karatu yaga sunan wannan kasar Africa a cikin jerin kasashen da suka shahara da karuwai.
Yara mata daga shekaru 12 suna karuwanci a kasar.
Da yake karuwan kasar basu yarda da amfani da kwaroron roba ba,
hakan kuma yasa aka samu kasar cikin kasashen da suka fi kamuwa da cutar kanjamau a duniya.
An dai danganta shigan mata karuwanci a kasar na Kenya ne saboda yadda kasar ke cikin talauci da tsadan rayuwa.
Na Takwas
Indonesia: Nanma dai sun haramta sana’ar karuwanci.
Amma cikin sauki zaka iya samun karuwai a kasar ta hanyar yanar gizo da kuma kawalan da suke hotel hotel na kasar da zasu kirawa mai bukata duk irin macen da yake so.
Saboda yadda ake shiga kasar domin yawon bude ido,
mata makotan kasar suna kwarara zuwa kasar domin su sayarwa mai bukata gabansu su samu abun duniya.
Na Tara
Spain: Itace kasar da tafi kowace kasa yawan karuwai a yammacin Turai.
Ita kasar ta Sifaniya ta baiwa karuwai daman suyi komai ba komai.
Garuruwan irinsu Bacelona, Madrid Ibiza cike suke da karuwai daga kudancin Amurka.
Hakanan kasar ta samar da tsaro a dukkanin unguwowin da ake harkar karuwanci a kasar, domin kiyaye lafiyan masu zuwa bukatarsu.
Harkar karuwanci a kasar dai ya samu tagomashi ne ganin yadda masu kudi suke zuba jarinsu,
su shiga kauyukan kudanci Amurka domin zakulo kyawawan yara su kawo su kasar suna sana’ar karuwanci.
Na Goma
Brazil: Babu dokar daya hana karuwanci a kasar,
babu kuma dokar da yace ayi. Don haka masu sana’ar suka cin karensu babu babbaka.
Sai dai kasar bata amince da karuwan tsayuwa akan titi ba, wanda hakan ya sabawa dokar kasar.
Karuwanci ya samu karbuwa ne a kasar ganin yadda suke da wuraren ziyarar gani da ido da ake zuwa daga kasashe.
Hakan nan suna da wani bukin da suke yi a duk shekara. Bukin da yake cikin bukukuwan duniya da suka shahara.
Bamu kawo muku wannan rahoton bane saboda mu tallatawa masu karatu inda karuwai suke ba.
Sai dai muna hakan ne saboda mutanen da basu tafiye tafiye, kuma basa karance karance,
amma idan sun tashi yin magana suke yi cikin jahilci da rashin sani.
Na ganin komai na rashin daraja Nijeriya ce kan gaba.
Da fatan zasu fahimci duk yadda suke yiwa Nijeriya kallon banza to tafi wasu kasashen a duniya.