Laifinsa kawai ya musuluntar da yarinyar da tace tana sonsa
Laifinsa kawai ya musuluntar da yarinyar da tace tana sonsa a Jihar Bayelsa.
Cirani ya tafi Jihar Bayelsa wata budurwa christian ta makale masa tana sonsa.
Saurayin ya gaya mata cewa bazai iya aurenta ba har saita musulunta.
Yarinyar nan ta amince za ta musulunta,
har takai ga amincewar saurayin ya dakkota, yazo da ita Jihar Kano inda aka musuluntar da ita.
Amma iyayenta da ‘yan uwanta sukace ya satota ne, kuma dan ta’adda ne, hakan yasa aka kamashi aka hukunta shi.
A yanzu dai maganar da akeyi Saurayin tuni aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru ashirin da biyar.
Tun kafin ayi wannan hukuncin, mun taba yin magana da wani lawyer,
har gidanmu yazo akan maganar Saurayin. Amma daga baya shima ya zare hannunsa.
Shugabanninmu na arewa fa babu wanda yace uffan, Buhari baiyi magana ba,
Senate president baiyi magana ba, sarkin musulmi bai yi magana ba,
da sauran masu ruwa da tsaki babu wanda yace uffan…
Wanne irin shugabanni muke dasu a kasar nan?
Shin ‘dan Arewa bai da ‘yanci kenan?
Ko kuwa bai da ikon yin magana?
Da suwa kuka fi samun yawan kuri’u?
Idan gudun tsira da kuri’unku ne yasa ku ke mana haka, to da suwa kuka fi samun kuri’u?
Tsoron me kukeyi da idan su aka taba kuke kokarin ganin kun hukunta ‘yan Arewa?