Hausa News

Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Datse Mazakutar Mijinta Da Wuka

Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Datse Mazakutar Mijinta Da Wuka A Jihar Taraba.

Wata matar aure mai shekara 25 ta datse mazakutar mijin ta a garin Tella da ke karamar hukumar Gassol na jihar Taraba.

Matar mai suna, Halima ta tafka wannan aika-aikan ne a ranar talata yayin da mijin ta, Umar Aliyu ke sharar barci.

Kanin wanda abin ya faru da shi, Shagari Umar, ya ce ihun Aliyu ne ya jawo hankulan mutane inda suka zo suka tarar da shi kwance cikin jini.

Umar yayi ikirarin cewa, “Mun ga matarsa Halima zaune a gefen gado rike da wukar da ta yi amfani dashi wurin datse mazakutar dan uwanmu.

Ya kara da cewa kiris ya rage fusattaun ‘yan uwan Umar da makwabta suyi mata duka,

amma manya sun shiga tsakani sunce a tausaya mata saboda tana dauke da juna biyu kuma suka kira ‘yan sanda.

A cewarsa “an garzaya da Aliyu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Jalingo mai nisar kilomita 150 daga garin Tella.

Ya ce, da isarsu asibitin, an bawa Aliyu kulawa cikin gaggawa aka tsayar da jinin da ke zuba daga raunin bayan an masa tiyata.

Likitan da ya kula da Aliyu, Dr Kyantiki Peter Adamu,

ya shaidawa manema labarai cewa an kirashi sashin wadanda ke bukatar kula cikin gaggawa don wani majinyaci da aka kawo bayan datse masa mazakuta.

Abinda mukayi shine tsayar da zubar jinin cikin gaggawa da kuma yi masa tiyata a inda aka masa rauni saboda ya rasa jini sosai kafin a kawo shi,” injishi.

Yace bisa ga dukkan alamu majinyacin zai murmure amma yan uwansa sun bukaci su tafi da shi saboda haka babu abinda asibitin zai yi a kai.

Shagari ya shaidawa manema labarai cewa cewa sun ɗauke Aliyu daga FMC Jalingo ne domin su tafi da shi wani asibiti a Gombe.

Mun dauke dan uwanmu daga FMC Jalingo mun tafi dashi FMC Gombe domin ya kara samun kulawar da yake bukata, inji Shagari.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP David Misal ya tabbatar da afkuwar lamarin,

ya kara da cewa ‘yan sanda sun kama Halima sun kuma fara binciken dalilin faruwar lamarin.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page