Kabilar Da Uwar Amarya Ke Kwana Da Ango Domin Tabbatar Da Kwazonsa
kabilar Banyankole: A mafi yawan kabilun nahiyar Afrika, ana dorawa kan mahaifiya alhakin fadakarwa dayin nasiha ga budurwar da za’a aurar.
A mafi yawancin lokuta, kanwar mahaifiya ce ke shirya budurwa domin ta fuskanci malubalen da ke cikin zaman aure.
Amma lamarin ba haka yake ba, a kabilar Banyankole da ke Kudu maso Yammacin kasar Uganda,
inda aka dorawa kanwar mahaifiyar budurwar da za’a aurar alhakin sanin namijin da za’a bawa auren diyar ‘yar uwar ta.
Babban aikin kanwar uwar budurwar da za’a aurar a kabilar Banyankole,
shine tabbatar da kuzarin ango ta fuskar saduwa kafin a kai ga aura masa diyar yar uwar ta.
Domin tabbatar da kuzarin angon, a wasu lokutan,
Kanwar mahaifiyar kanyi saduwar jima’i da angon diyar yar uwarta domin tabbatar da kwazonsa a gado.
Karin Bayani
Kazalika, kanwar mahaifiyar budurwar zata bawa angon tabbacin cewa diyarsu cikakkiyar budurwa ce da bata taba sanin wani da namiji ba.
Itace kuma ke da alhakin tabbatar da cewa diyarsu da zasu aurar bata taba sanin wani ‘da namiji ba,
ta hanyar duba tsiraicinta da yi mata binciken kwakwaf kafin aurar da ita ga saurayin da ke son aurenta.
A wasu lokutan, kanwar mahaifiyar kan kwana tare da ma’auratan a daren farko na aurensu,
domin ji da ganin yadda zasuci amarci, saboda kawai ta tabbatar da kuzarin angon da suka aurawa ‘diyarsu.
Duk da anayiwa wannan al’ada kallon tsohon yayi, ta nuna yadda kabilar Banyankole,
musamman masu yaren Bahima, suka bawa rike budurci muhimmanci.
Da zarar diyar ‘yan kabilar Bayankole ta cika shekaru 8 a duniya,
za’a fara saka mata matakai da takunkumi daban-daban domin fara yi mata shirin aure.
Duk da ‘yan kabilar Bayankole kan gudanar da al’adu dadan-daban yayin auren ƴaƴansu,
al’adar tabbatar da ƙwazon ango da budurcin amarya da ƙanwar mahaifiyar budurwa ke yi kafin kulla aure ta fi zama babban abun mamaki.