Hausa NewsNews

Tattalin arzikin Nigeria: Bashin da Nigeria take biya yafi karfin kudin da take samu

Nigeria

Hakika Nigeria tana cikin Wani mawuyacin Hali ta inda a shekaran 2022 bashin da take biyan bankin duniya yafi karfin kudin da take samu a Tattalin arzikin Nigeria.

Masu ruwa da tsaki a harkan tatalin arziki a Nigeria sune sukayi wan Nan kididdigan suka gano Nigeria tana cikin mawuyacin hali Kuma idan gomnatin Nigeria batayi da gaske ba za’a shiga Wani rayuwa Wanda Ba’a San irinsa ba.

Kamar inda kowa ya sani gomnatin Nigeria tana samun babban hanyar kudin shiganta ne ta hanyar man fetur da Kuma haraji.

Amma a lisafin na kudin da Nigeria tayi zata samu akan man fetur da gas wan Nan kudi Basu samu ba Kuma Hakan Yana da alaka ne da tallafin man fetur da gomnatin Nigeria take biya da Kuma masu fasa bututun man fetur din.

Masana tattalin arzikin Nigeria sunce idan har ana son a farfado da tatalin arzikin kasa to dole ne gomnatin Nigeria ta gaggauta cire tallafin man fetur, abin nufi fetur yayi tsada kenan.

Amma tabbas a yanzu haka danyen Mai Yana daraja sosai a kasuwar duniya amma ace har yanzu Nigeria Bata samun komai dashi, to Ina Kuma ga danyen Mai ya Fadi a kasuwar duniya abin zaifi haka lalacewa kenan.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page