Education
YAJIN AIKIN ASUU: Ba Dole Ne Sai Kowane Dan Najeriya Ya Yi Digiri Ba – Inji Gwamnan APC
YAJIN AIKIN ASUU: Gwamnan Jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso Gabas, David Umahi yace ilimin jami’a ba na kowa da kowa bane.
Umahi ya jadada cewa ba adalci bane ayi tsammanin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari taciyo bashin fiye da Naira tiriliyan 1 don biyan bukatun ASUU.
Gwamnan yayi wannan jawabin ne kan yajin aikin da malaman jami’o’i ke yi,
a lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga asusun ‘yan sandan Najeriya karkashin jagorancin Dr Ben Akabueze, a Abakaliki a ranar Laraba.