News

Wata Mata Ta Maka Mijinta A kotu Saboda Ya Buya A Bandaki Lokacin Da Yan Fashi Suka Shiga Gidansu

Wata Mata Ta Maka Mijinta A kotu Saboda Ya Buya A Bandaki Lokacin Da Yan Fashi Suka Shiga Gidansu

Wata mata mai suna Asiajo Oladejo ta kai karan mijinta a kotu bisa buya a bandaki lokacin da yan fashi su ka shiga gidansu.

Mrs. Oladejo, ta yi karar mijin nata mai suna Abidemi a gaban kotun majistire da ke Mafo a garin Ibadan, Jihar Oyo Najeriya.

Ta shaidawa kotun mijin nata ba abokin zama ba ne tun da ya kasa kare ta lokacin da bala’i ya afko musu,

inda take cewa sai dai ma yayi ta kansa ba ta iyalinsa ba.

Wata Mata Ta Maka Mijinta A kotu

Ta kara da cewa, ta shiga halin firigici a lokacin da yan fashin su ka shigo gidan nasu,

inda ta nemi mijin nata domin ya kawo musu dauki ya taimaka kesu ita da ya’yan ta (iyalansa),

amma ta neme shi ta rasa, a she yana cikin bandaki ya kulle kansa.

yan fashin sun yi abinda suka ga dama a gidan,

inda bayan sun tafi ne sai ga mijin nata Abidemi ya fito daga bandaki,

saboda haka take nema kotu ta raba auren nasu.

Ko da alkali ya wai-wayi wanda a ke karar, sai ya amsa cewa tabbas ya buya a bandaki,

amma ya bata hakuri, kuma ba yadda bai yi da ita ba akan ta dawo gidansa su cigaba da zama tare amma ta’ki.

Ya kuma roki kotu da ta bar masa ya’yan su guda uku a hannunsa,

inda yace kowa ya san cewa shi yana kuka da ya’yan sa.

Da take yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a SM Akintayo,

ta ki karbar korafin mijin nata, inda ta ce matar zata fi kulawa da su fiye dashi,

amma su biyun ne za su dauki nauyin karatun yaran, ta kuma raba auren nasu.

Yanzu dai bashi ba ita saidai Ya’yan da suke dashi, aure an riga an raba a kotu.

Also read: Petroluem Subsidy Conundrum – Nasir El-Rufai

HausaTiktok

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page