News

Gwamnatin Buhari ta nema iyayen dalibai da su roki ASUU ta janye yajin aiki

Gwamnatin Buhari ta nema iyayen dalibai da su roki malaman jami’a su jingine yajin aikin da sukeyi tsawon wata biyar saboda tayi abin da zata iya yanzu saura na iyayen dalibai.

Karamin Ministan kwadago Festus Keyamo ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyanata cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels a yammacin Jiya Juma’a.

Ministan yace “tun kafin kungiyar malaman ta ASUU ta fara yajin aikin gwamnati ta kira su don tattaunawa amma duk da haka sai da suka tafi yajin aikin.

Da aka tambaye shi ko me zai fadawa iyayen da yaransu ke cigaba da zaman gida har yanzu, sai ya ce:

“Zance musu suje su roke ASUU. Kamar yadda shugaban kasa ya fada a baya, wadanda suka sansu su rokesu don nuna kishinsu ga kasar.”

Ya cigaba da cewa “Me zamuyi fiye da haka? Tun kafin a fara yajin aikin muka kira su. Bawai kyalesu mukayi ba kawai muka kama barci.

Ba zai yiwu ka kyale mutum ya ci kwalarka ba kuma ya tilasta maka ciyo bashin naira tiriliyan daya.”

A farkon makon nan ne ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da mako hudu,

Kari a kan wata biyar da ta shafe bayan jingine aiki a jami’o’in Najeriya.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page