News

Yanda ake lalata damu a kasar saudiya

Yanda ake lalata damu: Wata ta bayyana yanda ake lalata dasu a kasar saudiya.

Inda ta fara bayani kamar haka

Sunan Aishatu Abubakar Anka, tace “Innalillahi wa inna illaihi raj’un, gareni da yan uwana da suke inda aka kaimu.

Tace wani bawan Allah ne yai mana hanya zuwa saboda mu sama aiki amma shima baisan haka abun dake faruwa ba.

Ya kawo mana a matsayin yan uwanshine akan zamuje saudiya, za kuma mu taimakawa musulunci da musulmai yan uwanmu da suke saudiya.

Sannan zamu dinga yin abinci wasu kuma su dinga share ka’aba wasu kuma zaa barsu a Madina, mukaji dadi mukayi hamdallah muka karba aikin.

Sai muka tafi Abuja akai mana interview,

ga tambayan da akai mana akan interview:

1. Kinyi Alkawarin zaki Taimkawa musulunci? Nace “Eh” zan taimakawa musulunci.

2. Kina da Aure? Nace “Eh, inada aure”.

3. Mijinki ya yarda? Nace mishi “Eh, mijina ya yarda”.

4. ‘Ya’yanki nawa? Nace mishi ‘ya’yana uku (3) na miji biyu mace guda daya.

5. Sai yace cikin yaranki naki waye karami? Nace namacen ce kuma shekarunta goma sha-shida (16 years old).

Sai yayi hamdalah yace babu matsalla, babu wata damuwa hajiya Aisha. Sai nace Ameen!

Daganan muka tashi muka tafi asibiti akayi mana test bayan wanda nayi na jiharmu.

Bayan anyi, sai muka dawo, akace zamu riga mahajjata zuwa. Shima nayi hamdalla sosai.

Munyi bankwana muna murna, ‘yan uwanmu na murna suma.

Sai aka kiramu akace zamu tashi ranan Alhamis, sai tafiya bata yuwu ba. Muna Abuja har ranar Lahadi.

Ranan lahadin kuwa jirginmu ya tashi daga Abuja zuwa Etopia.

Abin ya bamu mamaki, saboda mu bamusan Etopia zaaje ba ance mana saudiya.

Munanan sai aka tafi Etopia, Ni na taba yin ummara.

Sai naga wanda za’akaishi Saudiya me ya kaishi Etopia?

Daganan hankalina ya fara tashi, sai mutane sukace ai ba wani abu bane jirgin yawo ne.

Daga Etopia

Muna tashi daga Etopia sai Riyadh, sai aka kara mana motoci, agent din daya kaimu iyakanshi bakin airport.

Muka shiga motoci sai ya daga mana hannu, yace shi zai koma nigeria.

Daga zuwa aka tukamu, motan maza daban na mata ma daban.

Su maza suka jera da matansu bamusan inda akayi dasu ba, mu kuwa mukaje da motocinmu akace zamu wani gida.

Muna shiga cikin gidan hankalina ya tashi sai na fara fadin innalillahi wa inna ilaihi raj’un.

Mana nan, sai akace kowaccenmu ta kawo wayanta.

Sai nace me ya kawo amsan waya kuma?

Nan dai aka fara rigima, akace indai kawo waya. Gashi inajin kishin ruwa kuma sunce baza’a bani ba sai na basu wayata.

Abun ya bani mamaki matuka, nace wai mene dalilin sai na bada waya?

Akace aa babu komi kakida ne duk wanda ya shigo a amsa wayanshi.

Mutanen da kumazo muka tarar dashi duk an turasu an boyesu, ana korarsu da tsawa saboda kar mu gansu.

Hankalina ya tashi sai na dauki wayata na bada saboda inajin kishin ruwa,

bayan na bada wayar tawa sai suka bincika kayata daya bayan daya basu sama wata wayar ba.

Shikenan sai akace in shiga ciki, sai aka dibomun ruwan nasha.

Sai naje nayi fitsari nai tsarki na fito, abin yanata bani mamaki sauran mutanen kuwa sai cajesu akeyi.

Bayan an gama ne sai aka sayo mana gurasa da wani ruwan miya.

Hakanlinmu ya kara tashi saboda abin da bamu taba gani bane.

Daga cikin malaman asibiti da mukaje dasu, sai suka tsaya sukace su bazasu bada wayanau ba.

Karshe dai aka amsa wayoyin nasu. Sai aka kara tafiya asibiti akace za’a diba jinin a kara mana test.

Inda Aka ajiyemu

Bayan an gama sai muka dawo safiya ta waye sai aka kawo wani uniform da number a jikinsa, sai akace musa.

Ni inada number 5331 sauran mutane ma kowa da nasu. Duk safiya sai a kiramu a taramu a irgamu.

Munanan duk wanda aka kira ya fita bamu sake ganinsa, kuma shikenan ya fita. Abun sai yai ta bamu mamaki.

Bayan sati daya, sai ga wata mata wanda ana kiranta da Hajia Umma. Sai tazo.

Tana zuwa kuwa sai ta fadi ta suma, ai akayi sauri aka dagota ana mata fifita.

Daganan sai hankalinta ya dawo, sai muka tambayeta me ya faru? Sai tace wallahi tana cikin bala’i take.

Gidan da aka kaita gidan aiki larabawa ne kuma basa bata abinci.

Idan ta fara guga sai ta dauki kusan awa biyar tanayi bayan kuma ta wankesu.

Ta kara da cewa “ga guga, ga wanki kaya, ga wankin tiles, ga wankin bango sannan gana tolet kuma babu abinci”.

Daganan hankalinmu yafi na koyaushe tashi, sannan kuma gashi kara dibanmu ake.

Sai na tambaye ta kamar haka ” to wai ke idan kukaje kuna da daki ne?” Sai tace “wallahi hajiya dakin da aka bamu bema wuce in kin mike tsawonki. Nace innalillahi wa inna illaihi raj’un.

Sai na yanke shawara nace ni banzan shiga kamfani ba, inanan Allah ka rufamun asiri in samu inbar garin nan nidai hankalina ya tashi.

Mutanen nan kuwa suka cigaba da haka, sai rannan aka kira number ta.

Ranan Da aka fara kirani

Da aka kira number tawa sai aka tafi dani aka rabani da yan uwana, na rasa yadda zanyi.

Ina zuwa da yake an daukeni ranar juma’a ne sai ranane asabar sai aka bani body part akace zanje abaha.

Sai nace inje abaha yin me? Sai nace mata da turanci nifa bansan garin nan ba, sai take cewa ba matsala.

Ta daukoni kuma kamfani basusan inda za’a kaini ba, hankalina ya qara tashi matuka.

Na kira kamfani, kamfani sukaqi dauka. Sai na kira kanwar mamata nace kinji inda zaa kaini a lokacin sunje aikin hajji.

Tace to tayaya zaa daukoki ace zaa kaiki wata gari? Nace ban sani ba.

Tace tou kar ki yarda a tashi dake nan wajen, wasu suzo su daukeki indai kinga akwai zalunci. Nace to.

Na rokesu nace da Allah su mayar dani kamfani inata kuka, kuma shekarata 44 ina kuka ai kuwa kunsan balaci yayi bala’i.

Daganan sukayi haquri suka kaini kamfani, sai sukacema kamfani banida lafiya.

Kamfani kuwa tayita tambayata meke damuna? Nace ni bansan ciwota ba.

Aka kaini asibiti kusan sau uku (3 times) sai a tambayeni sai in ce musu ni bansan ciwona ba.

Sukace to bazasu kaini gida ba, inhar gida nakeso sai na biya kudi miliyan daya da dubu dari biyu (1.200,000).

Akwai wata tafinta da ake fada mata da larabci ta fassara mana, nace ta fada musu nace zan biya insha Allahu idan na dawo nigeria nayi alkawari. “Ina kuka a lokacin.”

Shikenan, sai daganan akwai sauran mutane don akwai wata Aisha Bala, ita kuma hadarin da ta shiga ita gidan boka musamman aka kaita.

Gashi matsafi kuma duk safe akwai tsintsayen da yake yankawa, hankalinta ya tashi.

Kuma rana daya muka dawo da ita, tana kuka ina kuka.

Tace mama aike kukanki karami ne, nifa gidan boka aka kaini. Nace Aisha Bala kiyi haquri haka Allah ya danganemu muyi haquri.

Yanda ake lalata damu

Da Allah a taimaka mata da addu’a mudai mun dawo, jama’anmu na neman addu’a acen. Saboda akwai yara kanana yan shekara 16 17 18 wanda su ana tafiya dasu ne ayi lalata dasu, wasuma gidan karuwai ake kaisu.

Wasu kuma akan kaisu gidan babba ne wanda bashi da mata su rika zama tare yana abin da ya kamata yayi da matarsa na sunna, wanda da zaran ya gaji da ita zaisa a canja mashi.

Kuma baban matsallan anakai yaran ne inda akafi karfinsu wanda akeyin musu dole da karfi da yaji ba yadda suka iya.

Akwai wasu yaranma da bamusan halin da suke ciki ba. (Yanda ake lalata damu)

Bayan munyi yarjejeniya dasu kan zan basu kudinsu aka kawo takarda nasa hannu.

Da saka hannuna saida nayi sati biyu ba’a waiwayeni ba. Sai rannan hankalina ya tashi na suma, mutane suka daukoni suka kaini kamfani, akace ayi haquri zaa kaini gida.

Akwai wata Hauwa’u yar gusau ce, itama anan wurin ta suma. Har aka dangwala hannunta batasan anyi ba na dauka tare zaa turomu sai aka turota ita kadai. Ta dawo gida ko bata dawoba ban sani ba.

Sai rannan akwai wata mata me cikin wata hudu cikin ya zube suma hankalalin kamfanin ya tashi.

Sai akace musa hannu mu uku a wata takarda, bayan munsa ne da daddare wajen karfe uku aka turomu gida. (Yanda ake lalata damu)

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page