Sirrin Aure

Aure bashi da anfani inji wata budurwa Zainab naseer Ahmad

Wata budurwa me suna Zainab naseer Ahmad tace Babu Wani anfani acikin aure sai yaudara da muzguna ma mace da Wasu mazan suke ma mata.

Zainab naseer Ahmad tayi wan Nan rubutu ne a shafinta na Facebook inda take cewa, hakika ita bataga Wani anfani acikin aure ba sai takura ma yarinya mace da akeyi.

Taci gaba da cewa aduk lokacin da yarinya budurwa ta fara tasawa Babu Wani Abu da iyayenta suke so sai suga sun aurar da ita badon komai ba sai don yanayi na lalacewar zamani.

Zainab naser Ahmad taci gaba da cewa ita aganin ta hakan be dace ba saboda ana Saka Yara mata ne kawai a cikin wahala.

Bawai Ina magana bane akan auren wuri a’a Ina magana ne akan auren gaba daya aure be zama dole ba, don haka za’a iya barin sa.

Ba Wani Abu akema aure ba sai Abu guda Daya don haka akwai Wanda zasu iya hakura da wan Nan abin Basu damu dashi ba, Hakan Yana nuna za’a iya rayuwa ba tare da aure ba ke Nan.

To malama Zainab naseer Ahmad mu abinda Muka sani a musulunci aure ibada ne Kuma aure Sunna ce ta manzon Allah.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page