News

Hukumar ‘Yan Sandan Nigeria haramta aibanta jami’ansu a fina-finai

Hukumar ‘Yan Sandan Nigeria: Sifeta Janar na Yan sandan Najeriya ya gargadi masu shirya fina-finai a kasar da su guji aibanta aikin dan sanda a shirye-shiyensu na talabijin, ba tare da izinin rundunar ba.

IG Usman Baba ya kara da cewa daga yanzu ka da a ƙara ganin wani mutum sanye da kayan ɗan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar. (Hukumar ‘Yan Sandan Nigeria)

Also Read: Danjarida Hausa series sabon Shiri me dogon zango na Abubakar Bashir me shadda

JAGWAL FASSARAR ALGAITA DUB STUDIO 2022

Ya ce idan ba haka ba to kuwa duk wanda ya karya doka zai ɗanɗana kudarsa.

Masu shirya fina-finai a Najeriya kan kwaikwayi jami’an yan sandan kasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.

Sanarwar da rundunar yan sandan ta fitar ta ce “ka da wani mai shirya fina-finai da ya sake nuna ƴan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar yan sanda.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ba za ta amince da bayyana aikin ɗan sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al’umma.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page