News

Gaskiya Ne Ana Zinace-Zinace A Ƙungiyar Shi’a (IMN) – Khadijah Mustapha Tsohuwar Ɗalibar Zakzaky

Gaskiya Ne Ana Zinace-Zinace A Ƙungiyar Shi’a (IMN) inji wata da ta taba zama a kungiyar.

Munga rubutun matar ne a inda take magana kamar haka:

Sunana Khadijah Mustapha kuma ni ‘yar asalin jihar Kaduna ce a ƙaramar Hukumar Giwa,

Sannan nayi tafiyar kungiyar Shi’a ta (IMN) karkashin Ibrahim Zakzaky tun daga shekarar 1990 – 2013.

Akwai maganganu da ake yawan yi akan neman Mata da fasikanci dasu a tsakanin mabiya Zakzaky a tsawon lokaci da ya haifar da surutai har wasu na ganin cewa karya ko sharri ake musu.

Ni da nake wannan rubutu Khadijah Mustapha cikakkiyar shaida ce akan haka,

Domin ni ‘yar cikin gida ce tsawon shekaru kafin Allah ya tsamar dani daga wannan mummunan hanya ta ɓata da hallaka,

Na wayi gari a yau a matsayin Musulma Ahlul Sunnah!

Shi'a
Shi’a ta IMN

Jan Hankali

Abin da yaja hankalina har nayi wannan rubutun shine,

Naga rubutu da wani yaro Matashi ɗan Shi’a mai suna Abdulhadi Aminu ya rubuta,

Yana nuna baƙin ciki da takaici akan yadda Zinace-Zinace ke ƙaruwa a tafarkin Zakzaky.

Daga baya Yaron ya janye rubutun da yayi sannan ya sake wani rubutun yana korafin an sauya akalar maganarshi zuwa wani wuri.

Nabashi uzuri kasancewar Yaro ne bai san dawar garin ba,

kuma ina kyautata zaton an yi mishi mazurai ne har ya ɗauki matakin da ya ɗauka na janye rubutun..

“Ina faɗi da babbar murya kowa ya sani fasadi da Mata a wurin Malaman Shi’a wannan ba komai bane!

Matan dake Shi’a sun san haka muddin za su fadi gaskiya,

Dayawa sun bar Shi’a saboda wannan matsalar”.

Hausatiktok

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page