Obi cubana Efcc ta kama shi a airport
Obi cubana Efcc: yaki da rashawa da cin hanci wato (EFCC) ta samu nasaran kama Pascal Okechukwu, Wanda akafi sani da Cubana Chief Priest
Obi cubana Efcc: Hukumar yaki da rashawa da cin hanci wato (EFCC) ta samu nasaran kama Pascal Okechukwu, Wanda akafi sani da Cubana Chief Priest akan zargin almundahana da karkatar da wasu makudan kudade.
Obi cubana Efcc Okechukwu, wanda aka kama a filin jirgin sama na Legas ranar Alhamis, jami’an yaki da cin hanci da rashawa na kasa (EFCC) sun tsare shi da wasu tambayoyi inda hukumar tace dama ta dade tana farautar wadanda suke yi masa aiki.
Tin bayan kama Okechukwu da hukumar yaki da rashawa da cin hanci tayi Bata bari kowa ya ganshi ba sai Yanuwan da family nashi kadai aka yarda dasu ganshi.
Amma ga dukkan alamu da inda hukumar yaki da cin hanci da rashawa suka nuna alamu za’a iya bada beli nashi a Cikin satin Nan.
Me magana da yamun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) Wilson Uwujaren, har yanzu bece komai akan maganar ba, Amma da wani labari ya samu zaku same shi daga wan Nan shafi namu.
In me karatu be manta ba Ankama Okechukwu bayan makwanni da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta tsare wani abokinsa Obinna Iyiegbu, wanda aka fi sani da Obi Cubana, bisa zarginsa da safarar kwayoyi.