News

Nura Khalid ya zage buhari akan rashin tsaro a arewa

Wan Nan shine cikakken video abinda malam nura Khalid ya fada akan shugaban kasa buhari.

Malam nura Khalid ya zagi buhari

Malam nura Khalid babban malami ne a wata babban masallaci dake cikin birnin garin Abuja, malam nura Khalid ya kasance me zafi wajen isar da Sako ko wani wa’azi ko hudubar juma’a.

Malam ya kasance me bawa gomnatin shugaban kasa buhari akan abubuwa na rashin tsaro da suke faruwa a kasar Nigeria musamman ma a yankin Arewacin Nigeria.

You can also read: azumin watan Ramadan 2022

Wai shin abinda nura Khalid ya fada gaskiya ne ko Kuma kazafi ne ko cin fuska ne ko Kuma zagi ne ga shugaba kasa buhari, me karatu Kaine alkalin wan Nan Abu da nura Khalid ya fada akan shugaban kasa buhari.

Hakika an mayar da Arewa Kamar ba’a Nigeria take ba an mayar da Arewa Kamar kwata mayankan dobbobi a sace wancen a harbe wancen a yanka wancen Kuma a duk lokacin da suka so.

Soda dama malam yayi ayani da Jan hankali akan irin abubuwan da suke faruwa a yankin Arewacin Nigeria ba Abu bane me kyau ya kamata gomnati ta dauka mataki.

Akoda yaushe malam bashi da wani magana a Cikin karatun sa ko hudubar sa sai na azauna lafiya da Kuma Kira da roko da Jan hankali akan gomnati ta Tina da Arewa akan harkan tsaro.

Akoda yaushe mutane suna ma Malam nura Khalid tsoron Kar wani Abu ya faru dashi ta inda yake ma gomnati Karan tsaye Yana fada mata magana duk inda yaga dama, dukda dai gaskiya ce Amma mutane suna Jin mishi tsoron hakan.

 

Malam Yana daya daga cikin malaman adinin musulunci Wanda bashi da tsoro wajen fadin gaskiya ko a Ina ne ta kama haka Kuma ko akan waye sabanin wasu malaman da suna ganin abubuwan da suke faruwa Amma babu Wanda yake fadin gaskiya da tinasarwa zuwa ga gomnati akan rashin tsaro da yake damun Arewa.

Video

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page