Rundunar sojan ruwa ta kora sojanta saboda aikata badala
Rundunar sojan ruwa na Nigeria tayi namijin kokari don ganin cire Bata gari daga cikin ta wan Nan dalilin yasa ta kora Daya daga cikin ma’ikatan ta domin Wani aikata lefi na badala da yayi.
Hakan ya biyo baya ne bayan kotun soji ta yanke masa hukunci akan wasu lefuka Daya aikata guda hudu.
Lefukan sune kamar haka, an an sama wan Nan sojin ruwa da yinkurin yin luwadi haka Nan ansame shi da rashin Jin magana haka Nan an same shi da rashin kunya da Raina na gaba dashi.
Bayan wan Nan kotun soji ta gama zayna mishi lefukan sa Nan take ta yanke masa zaman gidan kaso na shekara Daya da amsar kakin sa.
Hakan shi yake Kara nuna ma mutanen Nigeria dama duniya gaba daya hukumar sojin ruwa basa barin dukkanin wata barna a jikin su ko Kuma subar Wani ya aikata.