Sirrin Aure
ABUBUWAN DA KE JAWO MUTUWAR AURE A QASAR HAUSA
A wannan zamani da muke ciki musamman a kasar Hausa, akwai wadan su abubuwan da ke janyo mace-macen aure wanda ya zama ruwan dare gama duniya. A wani ittifaki da aka yi, an gano cewa Nijeriya ce ta biyu daga ciki kasashen suka fi matuwar aure. Kuma an gano cewa a Nijeriya Hausawa ne suka sami lamba ta daya wajen yawan sake-saken matansu.
Abubuwan da Ke Kawo Yawaitar Mutuwar Aure A Kasar Hausa:
Jahilci: Matsala ta farko da take jawo mace-macen aure a kasar hausa a wannan zamani ita ce jahilci da yawan mutanenmu musamman mutanen kauyuka, mun jahilci menene aure a mu’amalance da kuma a addinance. Da yawan matasa ba su san ka’idojin aure ba, ba su san hukunce-hukuncen aure ba, kai wallahi wasu ma ba su san ya ake yin wankan Janaba ba, amma a haka suke zuwa neman aure kuma a ba su.
Wallahi ko a cikin matasan birnin ma akwai wadanda da yawan su ba su san ilimin zamantakewar aure ba, ba su san me shari’a ta ce dangane da yawancin mas’alolin aure ba, kuma ba su san hakkokin matayensu a kansu ba. Su ma kansu matan yawanci ba su san hakkokin mazajensu a kansu ba. Yawancin abin da matasa suka dauka a matsayin aure shi ne, tunda na balaga, kuma na isa aure, shike nan bari in yi aure, sai in kawo abinci ta dafa min, ina da bukatar ta in je in biya, in ta yi ciki in tara kayan jego dana kauri, in ta haihu in siyo ragon suna, in na sake samun dama in kara aure in huta kawai abuna.
Su kuma yawancin ‘yan mata tunaninsu shi ne, ai an ce aure bautar Ubangiji ne, kuma kyan mace shi ne ta kasance a dakin mijinta, aikin mace kawai shi ne ta dafa wa mijinta abinci, ta biya masa bukatarsa na saduwar aure, ta yi ciki ta haihu, sai kuma ‘yan share-share da goge-gogen kayan daki. Wannan shi ne yawancin fahimtar da matasan wannan zamani suke da ita dangane da aure. Kuma a haka ake yin yawancin aurarraki a wannan zamanin ba tare da samun cikakken ilimi dangane da auren ba. Shi ya sa kuma hatta saki da ake yi a kan yi su a kan jahilci.
Mutanen birnin har wayau suna shiga cikin rikici da yawa sakamakon zurfin da suka yi a karatun Boko ba tare da ilimin addini ba, tare kuma da bin dokokin da yahudawa suka sa na Human Rights. Irin wadannan mutane da daman su sun bar dokokin Allah sun dau na yahudawa. Wannan ya sa na ce lallai jahilci da rashin sanin ilimin aure a addinance sun jawo mace-macen aure a kasar Hausa.
Kwadayi: Hausawa dai suna cewa “idan har da kwadayi, to da wulakanci”, kuma kowa ya hau motar kwadayi to zai sauka a tashar wulakanci. Da yawan mace-macen auren da ke faruwa a kasar Hausa suna biyo bayan kwadayi ne da ma’auratan suke sa wa a cikin zukatansu tun kafin su yi auren. Za ka ga iyayen yarinya sun dage da cewa dole su ‘yarsu sai mai kudi za ta aura, sai mai gida da mota da kaza da kaza. Itama yarinyar irin tunanin da take da shi kenan. Shi kuma saurayi, sai ya dage shi ala dole sai mace doguwa, fara, mai hanci, mai gashi mai kaza da kaza zai aura, wasu ma har da cewa ko da mayya ce.
Baya haka kuma, to yanzu kuma sai ga wata sabuwar masifar ta fito, ita ce, su ma yanzu mazan sun fara ikirarin cewa suma sai ‘yar Gwamna, Minista, Sanata ko kuma wani mai kudi zai aura. To shi irin wannan auren ko an yi shi bai cika karko ba saboda dama can ba don Allah aka yi shi ba.
Auren Dole: kowa dai ya san irin matsalolin da auren dole ya haifar kuma yake ci gaba da haifarwa a kasar nan. Sau da yawa nakan rasa inda tunanin wasu iyayen yake zuwa har su kasa gane ko fahimtar illar auren dole. Cikin kashi dari na auren dole da ake yi a kasar kashi casa’in daga ciki basa dadewa suke lalacewa, wasu ma har sai ta kai ga kisa.
Auren Zumunci: So da yawa auren zumunci idan ya zamana an yi shi ba tare da soyayya a tsakanin ma’auratan ba, to za ka cimma auren bai cika karko ba, dama-dama ma idan ya zamana akwai soyayya a tsakaninsu, to a kan samu wasu aurarrakin su daure, amma da wahala a wannan zamanin ka ga an yi auren zumunci ba tare da an samu matsala ba.
Auren Sha’awa: Auren sha’awa dai shi ne mutum ya auri wata mace don tana da tsayayyun nonuwa, baban kugu, dogayen kafafuwa, jar fata ko kuma wani abu makamancin haka. Ko kuma ita macen ta auri wani mutum saboda kyawun fuskar sa, saboda murdadden jikinsa, saboda tsayin gabobinsa ko kuma wani abu makamancin haka. To, a tarihi ma dai sam ba a taba samun wani aure da aka yi shi a kan sha’awa daya dore ba. Domin illar irin wannan auren shi ne, da zarar wadannan suffofi da aka yi auren domin su suka gushe, to shikenan matsala za ta fara aukuwa a auren daga nan sai rabuwa.
Rashin Tsafta: Sau da yawa ma’aurata suna yawan korafi dangane da rashin tsaftar da abokanan zaman su suke da ita. Wanda irin wannan yana jawo rabuwar aure. Wasu matan sam ba sa damuwa da tsaftar gidajensu, da jikinsu, da tufafinsu. Su ma wasu mazan ba sa kula da tsaftar jikinsu wanda hakan yana sa su gaji har a kai ga rabuwa. Son Zuciya: Da yawan ma’aurata su kan cutar da abokan zaman su haka kawai ba tare da wani dalili ko hakki ba. Wani mijin da gangan ya kan hana matarsa abinci ba wai don bashi da shi ba. Ko kuma ya ba ta mara dadi, shi kuma ya je waje ya ci mai dadi.
Ko kuma ita macen ta yi abinci ta zambada yaji alhalin ta san cewa mijinta ba ya son yaji. Ko dai wasu abubuwa makamantan haka. Wannan dalili tabbas yana jawo mutuwar aure.
Rashin Tawakkali: Idan har za a yi magana a kan dalilan da ke jawo mace-macen aure a kasar Hausa, to fa lallai ne rashin tawakkali ya shigo ciki. Domin a yau, musamman a irin halin da muka tsinci kan mu a ciki na karancin kudi da sauran kayan masarufi gami da tsadar rayuwa, Allah ne kadai ya san yawan auren da suka mutu a dalilin hakan. Wasu mutanen sam ba su da tawakkali, da zarar wani abu ya faru ko kuma wani abu ya faru da su sai hankalinsu ya gushe su kama daukar matakai irin wadanda suka saba da shari’ar Musulunci. Da haka sai ka ga ana ta samun matsaloli wadanda suka kai ga lalacewar aure.
Al’adu: Al’adunmu na gargajiya wadanda da yawan su sun ci karo da koyarwar addinin Musulunci, suma sun taimaka sosai wajen jawo mace-macen aure a kasar Hausa. Akwai abubuwa da yawa wadanda suke al’ada ce kawai ba addini ne ya wajabta wa ma’aurata yin su ba, ko kuma addini bai ce dole sai an yi ba, amma mu kuma sai mu dauke shi da zafi, a wasu lokutan ma mu nemi mu maida su shari’a ko kuma ma mu fifita su a kan abin da addini ya wajabta mana. Misali kayan lefe, gara da sauran su. Mugayen al’adu da bidi’o’i da muka daurawa kan mu sun taimaka matuka wajen janyo mace-macen aure a kasar Hausa.
Daga karshe, ina mai ba mu shawara da mu tashi mu nemi ilimin addinin Musulunci domin mu san yadda ake zamantakewar aure a bisa tsarin addini.